Jump to content

Naila Jaffri

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Naila Jaffri
Rayuwa
Haihuwa 1 ga Janairu, 1976
ƙasa Pakistan
Mutuwa Karachi, 17 ga Yuli, 2021
Sana'a
Sana'a ɗan wasan kwaikwayo, jarumi da dan wasan kwaikwayon talabijin
IMDb nm6585222

Naila Jaffri yar wasan kwaikwayo ce kuma darakta ’yar Pakistan.[1] An san ta da rawar da ta taka a wasan kwaikwayo Woh, Ek Kasak Reh Gayi, Mausam, Anaya Tumhari Hui da Tera Mera Rishta.[2]

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Naila a cikin 1965 a ranar 27 ga Janairu a Islamabad, Pakistan.[3]

Jaffri ta fara wasan kwaikwayo a kan PTV a shekarun 1980 kuma ta yi wasan kwaikwayo.[4]An santa da rawar da ta taka a wasan kwaikwayo Ek Mohabat Sau Afsaney, Sanam Gazida, Mujh ko Satana, Desi Girls da Thodi Si Khushiyan.[5] Bayan haka kuma ta fito a wasan kwaikwayo Kar Ka Kishi, Noorpur Ki Rani, Lamha Lamha Zindagi, Zeenat Bint-e-Sakina Hazir Ho da Sanjha.[6] [7] Tun daga nan ta fito a wasan kwaikwayo Surkh Jorra, Tera Mera Rishta, Aks, Anaya Tumhari Hui, Mausam, Ghalti, Marasim da Ek Kasak Reh Gayi.[8] [9] [10][11] Fitowarta na ƙarshe shine a Dushman a matsayin Durri wanda ya fara watsa shirye-shiryen bayan mutuwa a kan PTV.

rayuwar sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Naila ta yi aure amma bayan wani lokaci suka rabu[12]

Rashin lafiya da mutuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Naila ta kasance mai tsira da ciwon daji, kuma tana da ciwon daji na kwai.[13] [14] Ta rasu ne daga ciwon daji[15] [16] Ta rasu ne a ranar 17 ga Yuli, 2021, tana da shekaru 56. An yi jana’izarta a Masallacin Tooba da ke DHA Phase 2 Karachi kuma an binne ta a makabartar Sojoji da ke kusa da Kalapul, Karachi.

  1. "Veteran TV actress Naila Jaffri passes away". Geo News. 22 January 2021.
  2. Pakistani actors and royalties: A royal mess". Images.Dawn. 28 January 2021.
  3. "Actress Naila Jaffri passes away"
  4. Lahori Roots: Resurgence of theatre in the original hub of arts". The Express. 26 June 2021
  5. Naila Jaffri's call for help draws public ire". The Express Tribune. 24 February 2021
  6. Under Moheyyedin, the masters take the stage for an enthralling evening". The Express Tribune. 21 May 2021.
  7. "Pakistani celebrities launch 'give royalties to artists' campaign"
  8. "Curtain raiser: Napa International Festival kicks off in two days". Dawn News. 6 July 2021.
  9. Khan voices support to Naila Jaffri's demand over paying royalties". The News International. 14 July 2021
  10. "Powerful women glow differently: Yasir Hussain". The Express Tribune. 22 July 2021
  11. ئیں". Daily Jang News. 20 June 2022.
  12. "Peers praise art and philanthropy of Durdana Butt and Naila Jaffri". The News International. 18 August 2021.
  13. TV actress Naila Jaffri discharged from hospital". Dunya News. 18 September 2021
  14. Naila Jaffri passes way after long battle with cancer". Daily Jang. 12 September 2021.
  15. Veteran actress Naila Jaffri passes away". The News International. 14 September 2021.
  16. Remembering the best". The News International. 2 September 2021.