Jump to content

Naomi Nhiwatiwa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Naomi Nhiwatiwa
Rayuwa
Haihuwa Mutare, 15 ga Afirilu, 1941
Mutuwa 12 ga Afirilu, 2012
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa ZANU-PF

Naomi Pasiharigutwi Nhiwatiwa (15 Afrilu 1941 - 12 Afrilu 2012) 'yar gwagwarmayar samun 'yancin kai ta Zimbabwe ce kuma ministar majalisar ministoci. A cikin shekarar 1990s, ta yi aiki na tsawon lokaci a matsayin darekta tare da Hukumar Lafiya ta Duniya a Brazzaville, Kongo. [1] [2]

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife ta a Umtali (wanda aka sake masa suna Mutare a shekarar 1982), ta yi karatu a Amurka a Jami’ar Jihar New York da ke Buffalo, inda ta sami digirin digirgir a fannin sadarwa tsakanin al’adu da diflomasiyya a shekarar 1979. A ƙarshen shekarun 1970, ta halarci taron farko na kungiyar mata ta ZANU-PF a Shai Shai a Mozambique. Ta zama mai magana da yawun jam'iyyar, mai son inganta 'yantar da mata.[3] Bayan samun ‘yancin kai a ƙasar Zimbabwe a shekarar 1980, Nhiwatiwa na ɗaya daga cikin mata biyar da suka zama ‘yan majalisar dokoki a jam’iyyar ZANU-PF mai mulki. Tare da Joice Mujuru (daga baya mataimakiyar shugaban ƙasa tsakanin shekarun 2004 - 2014) da Victoria Chitepo, a matsayin mataimakiyar ministar aiyuka da sadarwa, ta kasance ɗaya daga cikin 'yan majalisar ministocin ƙasar Zimbabwe. [4]

A cikin shekarar 1988, ta bar gwamnatin Zimbabwe ta zama babbar jami'ar Unicef a Nairobi, Kenya. Ta koma Brazzaville a shekarar 1993 a matsayin darekta mai kula da hulɗar waje na Hukumar Lafiya ta Duniya na Yankin Afirka. A cikin shekarar 1998, ta zama babban mai ba da shawara ga Majalisar Ɗinkin Duniya a New York.

Bayan ta yi ritaya daga Majalisar Ɗinkin Duniya a shekara ta 2001, Nhiwatiwa ta zama ma’aikaciyar agaji, ta kafa gidan marayu na Zerapath AIDS a Harare. Ta kuma kasance malama mai ziyara a Jami'ar Pepperdine da ke California. Naomi Nhiwatiwa ta mutu a South Bend, Indiana, a ranar 12 ga watan Afrilu 2012.[4]

  1. "Naomi P. Nhiwatiwa". Palmer Funeral Homes. Retrieved 10 February 2016.
  2. "War hero Naomi Nhiwatiwa dies". New Zimbabwe. 23 April 2012. Archived from the original on 16 February 2016. Retrieved 10 February 2016.
  3. Lyons, Tanya (2004). Guns and Guerilla Girls: Women in the Zimbabwean National Liberation Struggle. Africa World Press. pp. 112–. ISBN 978-1-59221-167-8.
  4. 4.0 4.1 "Naomi Nhiwatiwa dies in USA". The Herald. 24 April 2012. Retrieved 10 February 2016. Cite error: Invalid <ref> tag; name "herald" defined multiple times with different content