Nesrine Malik

Nesrine Malik FRSL 'yar jarida ce 'yar asalin Sudan kuma marubuciya ce ta "We Need New Stories: Challenging the Toxic Myths Behind Our Age of Discontent (W&N, 2019)". Da yake zaune a Landan, Malik marubuciya ce na The Guardian kuma ta yi aiki a matsayin mai ba da shawara a shirin tattaunawar labarai na mako-mako na BBC Dateline London . [1]
Rayuwa ta farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Malik a Khartoum, Sudan, kuma ta girma a Kenya, Misira da Saudi Arabia . [2] Ta halarci Jami'ar Amurka a Alkahira da Jami'ar Khartoum a matsayin daliba, kafin ta koma Burtaniya a shekara ta 2004 don kammala karatun digiri a Jami'ar London.[2]
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Tare da aikinta a matsayin 'yar jarida, Malik ta shafe shekaru goma a kasuwannin masu zaman kansu masu tasowa.[3] Ta yi rubut game da siyasar Burtaniya da Amurka, siyasar ainihi da kuma matsanacin tsoron addinin musulunci. Maganganunta a cikin The Guardian bayan Harbi na <i id="mwQQ">Charlie Hebdo</i> an nakalto su a cikin mujallar New York da The New York Times, wani maudoo'i da ta kuma yi magana akai a shirin Newsnight na BBC tare da David Aaronovitch na The Times da Myriam François-Cerrah na New Statesman.[4] Rubuce-rubucen Malik, da kuma aika ga mujallar Foreign Policy suna mai da hankali ne kan siyasar Sudan.[5]
A cikin 2015, Malik da Peter Hitchens sun tattauna rawar da hijabi da al'adun Musulmi ke takawa a Burtaniya a tashar Channel 4 News . A cikin 2016, Malik na ɗaya daga cikin marubuta uku da aka nuna a cikin jerin "The Web We Want" na The Guardian suna tattauna Cin zarafin yanar gizo da maganganu marasa kyau da suka samu a kan yanar gizon game da aikinsu.[6] Baye da wannan, ta ba da gudummawa ga zaman a Majalisar dokokin Burtaniya tare da manufar magance tasirin cin zarafin kan yanar gizo akan marubutan da ke tasowa. [ana buƙatar hujja][<span title="This claim needs references to reliable sources. (September 2019)">citation needed</span>]
A cikin 2018, ɗan jarida Peter Oborne ya bayyana Malik a cikin British Journalism Review da rubutu kamar "tare da basira da dukar abin da ya shafi launin fata, aji, da jinsi, da kuma Islama". Oborne ya kasafta ta a matsayin misali ga ƙarni mai tasowa na 'yan jaridar Musulmi masu siyasa waɗanda "suna amfani da asalin su don haskaka rashin daidaito a cikin al'ummar Burtaniya. Sun amfani da Islama a matsayin asali a siyasa kamar yadda yake a addini. Kasancewa Musulunci yana ba wannan ƙarni na dubban masu tasowa murya ba na addini ba amma na bigirewar siyasa. A gare su, kayan aiki ne don nuna cewa Burtaniya ta kasance ƙasa da ke mamaye da kanan rukunia na mutane".[7]
A cikin 2019, Malik ta buga We Need New Stories: Challenging the Toxic Myths Behind Our Age of Discontent, wanda South African Sunday Times ya bayyana a matsayin littafi wanda "Malik tayi nazari da fassara ƙaryar da al'umma ta yarda da ita a matsayin gaskiya. " An sake shi a cikin takarda a cikin 2020, kuma an buga sabon bugu a cikin 2021.
A cikin 2020, ta bayyana a kan The Moral Maze a matsayin masu tattaunawa na muhawara da Michael Buerk ya shirya tare da Mona Siddiqui, Tim Stanley, Andrew Doyle; muhawarar ta kasance game da "halin kirkin Daular Burtaniya".[8]
Daraja da lambobin yabo
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin 2017, Diversity in Media Award ta zabi Malik a matsayin "Mai Jarida / Marubuta na Shekarar". A cikin wannan shekarar, an girmama ta a matsayin "Mai sharhin Al'umma da kuma banbance na shekarar" a Editorial Intelligence Comment Awards .
A cikin 2019, Gidauniyar Orwell ta sanya Malik a cikin jerin sunayen Orwell Prize saboda aikinta a kan "muguntar zamantakewa" na Burtaniya a cikin "tona asirin yanayin ƙiyayya".[9] A cikin 2019 da 2020, an sanya Malik a cikin jerin sunayen "Mai Bayani na Shekara" a kadamar da lambobi yabon Jarida ta Burtaniya.[10] A cikin 2021 Gidauniyar Orwell ta sake lissafa Malik don Lambar yabon Orwell don aikin jarida.
A cikin 2021, Malik ta sami lambar yabo ta Robert B. Silvers ta farko don aikin jarida.[11][12] An zabe ta a matsayin Fellow na Royal Society of Literature a shekarar 2023.
Bayanan da aka ambata
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Hill, Jane (22 April 2018). "Dateline London". BBC News – via Internet Archive.
- 1 2 "We need new stories". University of Sydney. Retrieved 25 October 2021.
- ↑ "Nesrine Malik". Curtis Brown. Retrieved 3 September 2019.
- ↑ Schuessler, Jennifer (4 May 2015). "Charlie Hebdo Award at PEN Gala Sparks More Debate". The New York Times. Retrieved 3 September 2019.
- ↑ "Nesrine Malik". Foreign Policy. Retrieved 17 May 2017.
- ↑ Cornish, Audie (29 April 2016). "'The Guardian' Launches New Series Examining Online Abuse". NPR.org. Retrieved 17 May 2017.
- ↑ Oborne, Peter (March 2018). "We do not Report Fairly on Muslims". British Journalism Review. 29 (1): 29–34. doi:10.1177/0956474818764596. ISSN 0956-4748.
- ↑ "Moral Maze, The Morality of the British Empire". BBC Radio 4. 25 July 2020. Retrieved 11 October 2021.
- ↑ "Nesrine Malik". The Orwell Prize. The Orwell Foundation. Retrieved 2 September 2019.
- ↑ "British Journalism Awards 2019 shortlist announced". Press Gazette. 5 November 2019.
- ↑ Caplan, Walker (5 January 2022). "Here are the winners of the inaugural Silvers-Dudley Prizes for criticism and journalism". Literary Hub (in Turanci). Retrieved 7 January 2022.
- ↑ "Winners of the Silvers-Dudley Prizes Revealed". Kirkus Reviews (in Turanci). Archived from the original on 7 January 2022. Retrieved 7 January 2022.