Neja

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Nijar (jiha))
Neja
Niger (en)


Suna saboda Nijar
Wuri
Map
 10°N 6°E / 10°N 6°E / 10; 6
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Minna
Yawan mutane
Faɗi 5,556,247 (2016)
• Yawan mutane 72.76 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 76,363 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Arewa maso yammacin jiha
Ƙirƙira 3 ga Faburairu, 1976
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa executive council of Niger State (en) Fassara
Gangar majalisa Niger State House of Assembly (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NG-NI
Wasu abun

Yanar gizo nigerstate.gov.ng
File:Minna,Niger state City gate.jpg
Jihar niger
Dutsen Zuma kenan na jikin Naira dubu dake a niger
Lambar mota kenan ta niger
babbar ƙofar makarantar kimiyya da fasaha

Jihar Neja Jaha ce dake Arewa ta tsakiyar Najeriya. Tana da yawan fili kimanin kilomita dubu saba'in da shida da ɗari uku da sittin da uku (76,363 ), da yawan jama’a kimanin miliyan uku da dubu ɗari tara da hamsin da huɗu da ɗari bakwai da saba'in da biyu, ƙidayar yawan jama'a na shekara ta (2006).Babban birnin jahar shine Minna.

Jihar Neja na cikin jihohi 36 na Najeriya Takenta shi ne '"Power State"' saboda tana da madatsun ruwa guda uku (3) da ke samar da kusan kashi 70% na wutar lantarkin Najeriya.

Kafawa[gyara sashe | gyara masomin]

An kafa jihar Neja ne a ranar 3 ga watan Fabrairun 1976 daga rusasshiyar jihar Arewa maso Yamma a zamanin mulkin Janar Murtala Mohammed.

Jihar tana a shiyyar arewa ta tsakiya mai yanki mafi girma wanda ya kai kusan 80000km2, tare da kusan kashi 70% na gonaki da noma. Jihar Neja tana iyaka da Jihar Zamfara ta ɓangaren Arewa, Yamma da Jihar Kebbi, Kudu da Jihar Kogi, Kudu maso Yamma da Jihar Kwara, Arewa maso Gabas da Jihar Kaduna da kuma Kudu maso Gabas da Abuja. Haka kuma jihar tana da iyaka ta ƙasa da ƙasa da jamhuriyar Benin tare da ƙananan hukumomin Agwara da Borgu zuwa Arewa maso Yamma.

Jahar ta Neja tana da manyan mutane da dama waɗanda suka riƙe manyan muƙamai a ƙasar Najeriya sannan jiha ce wacce ta ke da tsofaffin shugabannin ƙasa na Najeriya har guda biyu a lokacin mulkin soja, wato Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) mai ritaya da kuma Abdusalami Abubakar mai ritaya dukkaninsu mutanan Jahar ta Neja ne.[1][2]

Manyan Ƙananan hukomomin Jahar[gyara sashe | gyara masomin]

Manyan ƙananan hukumomin Jahar su ne kamar haka: Chanchaga, Bosso da kuma ƙananan hukumomin Bidda, Suleja da kuma Kontagora.

Yarukan Jahar[gyara sashe | gyara masomin]

Manyan yarukan jihar sun haɗa ne da Nufanchi, Hausa, Gbagi da kuma turanci inda yankunan Bidda da Agaie da kuma Lapai, Mokwa suka fi yawan masu amfani da yaren Nufanci, Yankin Kontagora, Kagara, Mariga, Mashegu Rijau, Suleja suke da mafi rinjayen masu amfani da yarukan Hausa. Paikoro, Chanchaga, Bosso, Edati da dai sauransu suna amfani da saura yarukan a matsayin masu rinjaye.

al'adar daka doya a jihar Niger

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai wuraren tarihi sosai a jahar ta Neja musamman a garin Zungeru inda kuma a nan ne turawan Yamma suka saka hannu domin haɗewan Najeriya ƙasa ɗaya daga sauran yankuna sannan a wannan garin ne gwamnan farko na Najeriya ya yada zango a matsayin hedikwata gareshi.

Alhaji Umar Farouk Bahago shi ne sarkin Minna.

Jihar Neja tana da iyaka da misalin jahohi shida, sune: Babban birnin tarayya, Kwara, Kogi, Kaduna(jiha)|Kaduna]], Kebbi kuma da Zamfara.[3]

Gwamnoni[gyara sashe | gyara masomin]

Jerin sunayen Gwamnonin jihar Neja. https://en.m.wikipedia.org/wiki/List_of_governors_of_Niger_State

Kananan Hukumomi[gyara sashe | gyara masomin]

Jihar Neja tana da Ƙananan Hukumomi guda ashirin da biyar (25). Sune:

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Jihar Neja na da manyan jami'oi na ilimi waɗanda suka haɗa da:

Jami'o'i a jihar Neja[gyara sashe | gyara masomin]

Yaruka[gyara sashe | gyara masomin]

An jero yarukan jihar Neja dangane da ƙananan hukumomin da ake amfani da su;[13]

LGA Languages
Agaie Nupe, Dibo; Kakanda;
Agwara Cishingini
Bida Nupe, BassaNge, Gbari
Borgu Busa, Bisã; Boko; Cishingini; Laru; Reshe
Chanchaga Basa-Gumna; Bassa-Gurmana; Gbagyi; Gbari; Nupe; Kamuku; Tanjijili
Edati Nupe, BassaNge
Gbako Nupe
Gurara Gwandara, Gbagyi
Katcha Nupe, Dibo; Kupa
Kontagora Acipa, Eastern; Asu; Tsishingini; Tsuvadi
Lapai Nupe, Dibo; Gbari; Gupa-Abawa; Kakanda; Kami;
Magama Lopa; Tsikimba; Tsishingini; Tsuvadi
Mariga Baangi; Bassa-Kontagora; Cicipu; Kamuku; Nupe; Rogo; Shama-Sambuga; Tsikimba; Tsishingini; Tsuvadi
Mashegu Asu; Tsikimba; Tsishingini; Nupe-Tako
Minna Nupe; Gbari; Gbagyi
Mokwa Nupe, Yoruba; Gbari
Munya Adara
Paikoro Gbari; Kadara
Rafi Basa-Gurmana; Bauchi; Cahungwarya; Fungwa; Gbagyi; Gbari; Kamuku; Pangu; Rogo; Shama-Sambuga
Rijau Fulani; C'Lela; Tsishingini; Tsuvadi; ut-Hun
Shiroro Gbagyi; Gurmana; Bassa
Suleja Gbagyi; Gbari; Gwandara; Nupe; Tanjijili
Wushishi Hausa; Nupe; Gbari

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kainji Lake National Park". United Nations Environment Programme: World Conservation Monitoring Centre. Archived from the original on 30 September 2007. Retrieved 21 October 2010.
  2. "Boko Haram ta mamaye garuruwa da dama a jihar Neja". BBC. 4 October 2021. Retrieved 10 October 2021.
  3. "Niger | state, Nigeria". www.britannica.com.
  4. Keetu (19 August 2017). "List Of Accredited Courses,Offered In Federal Polytechnic Bida (Fed Poly Bida)". Retrieved 26 August 2021.
  5. https://schoolings.org/list-of-accredited-courses-offered-in-federal-polytechnic-bida-fed-poly-bida/
  6. "Updated List of Courses Offered In FUTMINNA forJAMB 2021,Registration". O3schools. 5 March 2021. Retrieved 26 August 2021.
  7. https://tribuneonlineng.com/ibb-university-vc-visits-oil-exploration-site-at-gulu-commends-nnpc/
  8. https://tribuneonlineng.com/provost-fce-kotangora-bags-kidcs-award-of-grand-commander-of-intellectual-discourse/
  9. "Niger State School of Nursing Gets Full Accreditation – THISDAYLIVE"
  10. "Niger State School of Nursing Gets Full Accreditation – THISDAYLIVE"
  11. "Eyagi Community jubilates as Government Technical College in Bida, Niger State receives furniture from MTN Foundation"
  12. https://gazettengr.com/buhari-regime-spends-n106-million-to-construct-college-hall-in-minna/
  13. "Nigeria". Ethnologue (22 ed.). Retrieved 26 August 2021.


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara