Jump to content

Noma a kasar Gambia

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Noma a ƙasar Gambia Noma yana da kaso mai tsoka a cikin taskar tattalin arzikin ƙasar Gambia, wanda ya ƙunshi kashi 25% na tattalin arzikin ƙasar.[1] Kusan kashi 75% na ma'aikata a ƙasar Gambia suna aiki ne a cikin masana'antun noma. Manyan amfanin gona da ake samarwa a ƙasar su ne;  Gyaɗa , Gero, Dawa, Mangwaro,  Masara, ridi, ƙwayar dabino, da kuma Yazawa.  Babban amfanin gona da ake samarwa a ƙasar shi ne Shinkafa.

Duk da kasancewar noma wani babban yanki a cikin tattalin arzikin ƙasar Gambia, amma har yanzu matsalar abinci, matsalace da ta addabi al'ummar ƙasar. Abubuwan amfanin gona kawai suna samar da kusan kashi 50% na abinda al'ummar ƙasa ke bukata saboda ƙarancin amfanin gona. Da yawan jama'a sun dogarane sosai kan shinkafa, suna buƙatar metrik ton 398,364 a kowace shekara. Amma ƙasar Gambia abinda da ke iya samarwa kawai shi ne 22,706 metrik ton na shinkafa a kowace shekara. A sakamakon haka, tana buƙatar ta shigo da kusan kashi 80-90% na shinkafar da take bukata kowace shekara.

Ko da yake kusan kashi 45% na ƙasar noma a Gambiya ana amfani da ita wajen noman gyada, yawancin gyadan da ake nomawa ana fitar da ita ne zuwa ƙasashen waje, abin da ke ƙara haifar da rashin abinci.

https://en.m.wikipedia.org/wiki/Agriculture_in_the_Gambia

  1. https://jems.sciview.net/index.php/jems/article/view/92