Olufemi Adebanjo
Olufemi Adebanjo | |||||
---|---|---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 - District: Alimosho
6 ga Yuni, 2015 - | |||||
Rayuwa | |||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Harshen uwa | Yarbanci | ||||
Karatu | |||||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Olufemi Adebanjo (an haife shi a ranar 12 ga watan Yuni, na shekara ta 1961) ɗan siyasan Najeriya ne wanda a halin yanzu yake zama ɗan majalisar wakilai ta tarayya a majalisar dokokin Najeriya ta 9 . Yana wakiltar mazabar Alimosho a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC). Shi ne mataimakin shugaban kwamitin raya karkara a majalisar wakilai ta tarayya har zuwa watan Mayu 2023. [1]
Rayuwar farko da aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Olufemi Adebanjo ya girma ne a jihar Legas, Najeriya . [2] A cikin shekara ta 1980, ya sami takardar shedar makaranta daga Makarantar Methodist inda ya halarci Jami'ar City, New York (Amurka) yana samun digiri na farko a fannin tattalin arziki.
Sana'ar siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Adebanjo ya fara harkar siyasa ne a matsayin ɗan siyasa na asali a shekarar 1999 lokacin da aka zabe shi a majalisar dokokin jihar Legas mai wakiltar mazaɓar Alimosho 01 a karkashin jam’iyyar siyasa ta Alliance for Democracy (AD). Daga nan ya rike mukamai daban-daban a jihar Legas, ciki har da zama babban sakataren karamar hukumar Alimosho a shekara ta 2003, shugaban ƙaramar hukumar Alimosho a shekara ta 2004, da kuma mai ba gwamna shawara na musamman kan kafa da horaswa a lokacin gwamnatin Babatunde Fashola a shekara ta 2007. zuwa shekara ta 2011. [3] A zaben shekara ta 2015, ya tsaya takarar ɗan majalissar wakilai ta tarayya a karkashin jam’iyyar APC kuma ya samu nasarar zama wakilin mazabar Alimosho ta tarayya. [4] A zaben ‘yan majalisar wakilan Najeriya na 2019 da aka gudanar a jahar Legas, ya doke dan takarar jam’iyyar PDP Akinwale Akinsanya da wasu ‘yan takarar jam’iyyar 14 inda ya ci gaba da rike kujerarsa a majalisar wakilai ta tarayya. Adebanjo ya gabatar da kudiri game da bala’in gobara da ya afku a mazabarsa, wanda ya yi sanadin asarar rayuka 5. Mummunan tashin gobarar dai ya biyo bayan barnatar da bututun man ne da wasu ‘yan daba suka zo da tirela har ma ‘yan sanda suka ba su kariya yayin da suke aikata wannan haramtacciyar hanya. [5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Chairmen and Deputies of Standing and Special Committees in the 9th House of Representatives" (PDF). PLAC. July 2019. Archived from the original (PDF) on 2023-06-14. Retrieved 2023-03-23.
- ↑ "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". nass.gov.ng. Retrieved 2023-03-24.
- ↑ name="nass">"National Assembly | Federal Republic of Nigeria". nass.gov.ng. Retrieved 2023-03-24."National Assembly | Federal Republic of Nigeria". nass.gov.ng. Retrieved 2023-03-24.
- ↑ "Biography Of Olufemi Adebanjo". Media Nigeria. 2018-06-07. Retrieved 2023-03-23.
- ↑ "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". www.nass.gov.ng. Retrieved 2023-03-24.