Omar Shegewi
Appearance
| Rayuwa | |
|---|---|
| Haihuwa | Libya, |
| Mutuwa | 1928 |
| Yanayin mutuwa | hukuncin kisa (rataya) |
| Ƴan uwa | |
| Abokiyar zama | Zuhra Ramdan Agha Al-Awji (mul) |
| Sana'a | |
| Sana'a | revolutionary (en) |
| Imani | |
| Addini | Musulunci |
Omar Shegewi (Arabic: عمر الشغيوي;)[1] ya mutu a shekara ta 1928) shi ne jagoran juyin juya hali ɗan gwagwarmaya na ƙasar Libya wanda ya yi yaki da 'yan mulkin mallaka na Italiya a Libya a lokacin yakin Italo-Senussi na biyu.[1] Shegewi ya fito ne daga garin Hun da ke tsakiyar ƙasar Libya. Sojojin Italiya ƙarƙashin jagorancin Rodolfo Graziani sun yanke masa hukuncin kisa tare da kashe shi ta hanyar rataya bayan yakin Afia.[1] Ya auri Zuhra Ramdan Agha Al-Awji (Arabic: زهرة رمضان آغا العوجي) kuma sun haifi ‘ya’ya uku: Mohammed Shegewi, Hassan Shegewi da Idris Shegewi.[1]