Jump to content

Paloma del Rana

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Paloma del Rana
Rayuwa
Haihuwa Bioko, 20 century
ƙasa Gini Ikwatoriya
Mazauni Ispaniya
Karatu
Harsuna Yaren Sifen
Sana'a
Sana'a marubuci da mawaƙi
Mamba Hijas del Sol (en) Fassara
Sunan mahaifi Paloma del Sol

Paloma Loribo wacce aka fi sani da Paloma del Sol, mawaƙiya ce 'yar Equatorial Guinea, mai kiɗa, mai zane, 'yar wasan kwaikwayo kuma marubuciya.

An ta a tsibirin Bioko, ta rayu a Sifaniya, kuma shahararriya ce musamman saboda kasancewa ɗaya daga cikin membobin duo, Hijas del Sol.[1]

Paloma ta shiga duniyar waka a Equatorial Guinea ne tun tana ƙarama, kodayake nan da nan, a shekarar 1992, bayan ta yi wasa tare da gwaggwanta Piruchi Apo Botupá a wajen Bikin Waƙoƙin ƙasar Sifaniya wanda Cibiyar Al'adun kasar Sifaniya ta Guinea ta shirya, inda suka lashe kyaututtuka don waƙoƙin asali mafi kyawu da kuma mafi kyawun wasan kwaikwayo inda suka yi tafiya zuwa Spain don Bikin Expo '92 kuma a wannan shekarar ta shiga wasan Bikin OTI tare da gwagwanta Piruchi apo . [2]

Tun daga wannan lokacin sun kafa ƙungiyar waka su biyu "Hijas del Sol".[3] Amma bayan da suka rabu a shekara ta 2006, Paloma ta yanke shawarar yin hutu daga waka kuma ta mai da hankali kan wasu fannoni, kamar zane da rubutu. Ta yi bikin nune-nunen hotuna da yawa kuma ta rubuta littafinta na farko, Cuentos Africanos. [4]

Ta kuma je yawon shakatawa a Canary Island, a matsayin mai bada labari. A matsayinta na mai zane Paloma del Sol ta fara zane a alif 1995. Ta fara bayyana sha'awowinta na kusa, abubuwan da ta fi so. Zanukan kurciya da hotuna ma'adanan Afurka.[5]

A karshen shekara ta 2010, Paloma del Sol ta buga albam dinta ita kaɗai na farko mai suna Goza de la Vida.[6] Ta kuma wallafa sabon littafi mai suna La batalla de los Dioses,[7] kuma ta cigaba da shirya bikin nunin zanukan ta a ɗaukacin ƙasashen Sifaniya.

A cikin shekara ta 2013, ta wallafa littafin nobel dinta mai suna asos Desconocidos, wanda ya zamanto babban nasara wajen sayarwa, wanda ya sa ta wallafa bugu na biyu. A cikin shekara ta 2015, ta wallafa nobel mai suna Momentos Fugaces.

A cikin watan Afurelun 2016, ta saki albam dinta na biyu mai suna Atrévete a ser Feliz, da wakoki a cikin harshen Bubi da kuma a Sifaniyanci wanda ya zamo wakan da ya zama taken albam din da kuma wani sashe na wakokin fim din Relaxing Cup of Coffee, fim din da ta fito kuma a matsayin jaruma, kuma an gabatar da ita don kyautar Wakar Asali ta Musamman a bikin Lambar Yabo na Goya a cikin shekara ta 2017.[8]

  1. Artist Biography by AllMusic
  2. "Nubenegra.com". nubenegra.com. Retrieved 24 July 2017.
  3. Extracto del artículo publicado en El Pais Semanal en diciembre de 2.001. (in Spanish)
  4. Paloma Loribo, la luz africana (in Spanish)
  5. Paloma Loribo, de Las hijas del Sol, expone sus obras en Ármaga Archived 2019-02-10 at the Wayback Machine (in Spanish)
  6. Paloma del Sol: "No tengas miedo a las dificultades de la vida" (in Spanish)
  7. Paloma retoma el vuelo (in Spanish)
  8. Relaxing Cup of Coffee 17 Candidaturas (in Spanish)