Jump to content

Patrice Désilets

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mukala mai kyau
Patrice Désilets
Rayuwa
Haihuwa Saint-Jean-sur-Richelieu (en) Fassara, 9 Mayu 1974 (50 shekaru)
ƙasa Kanada
Karatu
Makaranta Jami'ar Montréal
Sana'a
Sana'a game designer (en) Fassara da creative director (en) Fassara

Patrice Désilets (an haife shi ranar 9 ga watan Mayu, 1974) ɗan ƙasar Kanada ne, mai kirkirar wasan kwamfuta, wanda aka fi sani dalilin ƙirƙiro jerin wasan kwamfuta na Assassin's Creed. Ya yi aiki a matsayin darektan kirkiro Assassin's Creed, Assassin-Creed II, da Assassin 'Cree: Brotherhood. An kuma san shi dalilin kasancewarsa darektan da ya bayar da umarnin ga kamfanin da ke wallafa wasannin kwamfuta watau Ubisoft a lokacin samar da wasan kwamfuta mai taken, Prince of Persia: The Sands of Time. A shekarar 2014, ya kafa gidan wasan kwaikwayo a Kanada na Montreal, inda ya yi aikin samar da wasan kwamfuta na Ancestors: The Humankind Odyssey.

Farkon rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a shekara ta 1974 a Saint-Jean-sur-Richelieu, Quebec, Désilets ɗan Jacques Désilets ne, masanin lissafi kuma darektan kwalejin CEGEP, da Luce de Bellefeuille, Darakta Janar na Sakatariyar Kula da Kasa da Kasa. A shekara ta 1996, Désilets ya sami digirin farko a fannin nazarin fina-finai da adabi a Jami'ar Montreal, wanda a lokacin da ya gabata, ya shiga kwalejin Collège Édouard-Montpetit.[1] Da yake ya fito daga cikin ahalin ƴan fim, ya yi amfani da ta shi hikimar wajen tsara shirya wasannin da ya ɗauki jagorancin ƙirƙiro su ciki har da wasan kwamfuta na Assassin's Creed da aka fitar a shekarar 2007 da kuma Assassin-Creed II wanda aka saki a shekarar 2009. Désilets ya samu yabo da kyaututtuka dalilin ƙirƙiro wasannin kwamfuta da su ka haɗa da: Assassin's Creed: Brotherhood, Prince of Persia: The Sands of Time, Disney's Donald Duck: Goin' Quackers, da Hype: The Time Quest.[2]

Ubisoft da TGQ

[gyara sashe | gyara masomin]

Barin yi wa kamfanin Ubisoft aiki

[gyara sashe | gyara masomin]
Patrice

Désilets ya bar kamfanin Ubisoft a watan Yunin 2010, wanda kamfanin ya tabbatar da hakan a ranar 13 ga watan Yuni, 2010. Bayan shekara guda daga barin masana'antar shirya wasan kwamfuta, Patrice Désilets a hukumance ya kuma shiga wani kamfanin shirya wasan kwamfuta ɗin na THQ a matsayin Darakta a watan Yunin shekarar 2011. [3] Shekaru biyu a THQ Montreal, Désilets yana aiki a sabon wani furojet-(project ) da akai ma taken 1666 Amsterdam, inda ya ke jagorantar wasu ma'aikatan ma'aikatar kusan mutane hamsin.

[4]

Kamfanin THQ, ya samu fatara a shekarar 2012. Daga bisani kamfanin Ubisoft ya sayi THQ Montreal, a shekarar 2013.

Patrice Désilets, mai tsara gami ko shirya wasan kwamfuta, Ubisoft ta sallame shi a shekara ta 2013 saboda takaddamar kwangila. Désilets ya yi iƙirarin cewa an kore shi ba bisa ƙa'ida ba kuma yana shirin kwatar haƙƙinsa daga kamfanin na Ubisoft.

Bayan wannan, Désilets da Ubisoft sun cimma yarjejeniya a watan Afrilun 2016 inda Désilets ya dawo da dukkan hakkoki na ikonsa ga aikin da ya ke yi ko furojet-(project) ɗin 1666 Amsterdam.

Panache Digital Games

[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 14 ga watan Disamba, 2014, Désilets da tawagarsa sun ƙaddamar da sabon ɗakin ci gaba da aikin shirya wasan kwamfuta a Montreal da ake kira Panache Digital Games.[5] Sun kaddamar da wasan kwamfutar su na farko, Ancestors: The Humankind Odyssey a shekarar 2019.[6]

Shekara Suna Wanda ya ƙirƙiro
1999 Hype: The Time Quest Ubi Soft Montreal
2000 Donald Duck: Goin' Quackers
2003 Prince of Persia: The Sands of Time Ubisoft Montreal
2007 Assassin's Creed
2009 Assassin's Creed II
2010 Assassin's Creed: Brotherhood
2019 Ancestors: The Humankind Odyssey Panache Digital Games
  1. "University of Montreal, Montreal, Quebec(QC)". Classmates.com. Retrieved 2013-10-03.
  2. "Patrice Désilets". MobyGames. 2006-11-14. Retrieved 2013-10-03.
  3. Curtis Brunet (2010-10-19). "Patrice Désilets Returns to Games; Joins THQ Montreal". TotalActionAdventure.com. Archived from the original on 2013-10-04. Retrieved 2013-10-03.
  4. "Game designer Patrice Desilets fired, intends to 'fight Ubisoft vigorously'". Polygon. 2013-05-07. Retrieved 2013-10-03.
  5. Futter, Mike (November 12, 2014). "Original Assassin's Creed Creative Director Patrice Désilets Announces Panache Digital Games". Game Informer. Archived from the original on July 4, 2015. Retrieved May 12, 2015.
  6. Kato, Matthew (April 23, 2015). "Patrice Désilets' New Game Explores Mankind's Greatest Achievements". Game Informer. Archived from the original on April 25, 2015. Retrieved May 12, 2015.