Jump to content

Paulos Tesfagiorgis

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Paulos Tesfagiorgis
Rayuwa
Haihuwa Eritrea, 20 century
ƙasa Eritrea
Karatu
Makaranta McGill University
McGill Faculty of Law (en) Fassara
Sana'a
Sana'a university teacher (en) Fassara
Employers University of Asmara (en) Fassara
Kyaututtuka

Paulos Tesfagiorgis ɗan gwagwarmayar kare hakkin dan adam ne na Eritrea . Ya kafa Cibiyar Yankin Kare Hakkin Dan Adam da Ci Gaban Jama'a (PFDJ) mai lasisi a Eritrea. Tesfagiorgis ya kuma kasance co-kafa kuma shugaban kungiyar Eritrean Relief Association a lokacin yakin neman 'yancin kai na Eritrea . [1]

A lokacin ‘Yakin Independence na Eritrea, Paulos Tesfagiorgis shi ne shugaban Ƙungiyar Taimakon Eritrea, inda yake tsara taimakon ƙasa da ƙasa ga ‘yan Eritrea, musamman a lokacin yunwar 1983–1985 a Habasha. Bayan samun ‘yancin Eritrea, an nada Tesfagiorgis a kwamishin da ya ƙirƙiri kundin tsarin mulkin Eritrea. An amince da kundin tsarin mulkin ne a shekarar 1997. A shekara ta 2002, Tesfagiorgis da wasu ‘yan Eritrea 17 suka kafa ƙungiyar Citizens Initiative for the Salvation of Eritrea (CISE)[2]

Ra'ayoyin siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin takardarsa mai suna A Personal Observation, Tesfagiorgis ya wallafa wani labari mai taken “Me Ya Yi Kus-kure?: Ƙungiyar ‘Yantar da Mutanen Eritrea daga Yaki Zuwa Mulkin Jiha.” A cikin wannan rubutun, Tesfagiorgis ya bayyana ra’ayinsa game da siyasa da Dimokuradiyya ta hanyar nazarin yadda Ƙungiyar ‘Yantar da Mutanen Eritrea (EPLF) ta canza daga rundunar ‘yantarwa zuwa gwamnatin danniya. EPLF ta fara ne da nasara wajen haɗa ƙungiyoyin Eritrea don yakar mamayar Habasha. Sai dai takardar ta nuna cewa a ƙarshen yakin ‘yanci, EPLF ta gaza samar da dimokuradiyya bayan yakin. An takaita ra’ayin siyasa da kuma ‘yancin ‘yan jarida, abin da ya sa da dama daga cikin ‘yan Eritrea suka tsere daga ƙasar. Tesfagiorgis ya kammala da cewa gazawar EPLF wajen daidaita wa sabon yanayin zaman lafiya da kuma ayyukan shugaban ƙasa sun haifar da mulkin danniya da kuma ruguza burin samun Eritrea mai ‘yanci da ci gaba. [3]

Ya yi imani cewa gwamnati kawai waɗanda aka zaɓa ta dimokuradiyya ne suke da sahihanci, saboda koyaushe suna ɗaukar alhakin ga mutanen da suke mulkawa. Saboda wannan dalili, shi ma ya guji tashin hankali.[4] A shekarar 2018, ya shiga ƙungiyar masu fafutuka marasa son ra’ayi ta Eritrea Focus dake Burtaniya domin inganta sauyin mulki na dimokuradiyya ba tare da tashin hankali ba.[5]

  1. "Paulos Tesfagiorgis". Archived from the original on 2018-08-15. Retrieved 2018-08-14.
  2. "Paulos Tesfagiorgis". Archived from the original on 2018-08-15. Retrieved 2018-08-14.
  3. what went wrong
  4. Believes
  5. https://www.eritrea-focus.org