Jump to content

Proscovia Nalweyiso

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Proscovia Nalweyiso
Rayuwa
Haihuwa Rakai District (en) Fassara, 1 ga Yuni, 1954 (70 shekaru)
Mazauni Entebbe (mul) Fassara
Sana'a
Sana'a soja

Proscovia Nalweyiso, babbar jami'ar sojan Uganda ce a rundunar sojojin Uganda (UPDF). [1] A matsayi ta Laftanar-Janar, ita ce mace mafi girma a matsayin jami'in soja, a cikin sojojin Uganda. [2] [3]

An haife ta a watan Yuni 1954, a gundumar Mpigi, a cikin iyali mai yara 20. [1] [3] A cikin shekarar alif dubu daya da dari tara da saba'in da Tara 1979, ta fara aiki a matsayin malamar makaranta da buga rubutu a yankinta. A wannan lokacin, ta zama memba mai ƙwazo a Jam'iyyar Demokraɗiyya ta Ugandan. [1] [3]

Bayan zaɓen ƙasa na Uganda na shekarar 1980 da kuma kafa kungiyar Resistance Army (NRA), Nalweyiso ta shiga cikin daji a cikin shekarar 1982. [1] [3]

A cikin shekarar 1983 an kafa wata ƙungiya ta mata mayakan NRA kuma an naɗa Nalweyiso a matsayin kwamandanta. A shekara mai zuwa, an ƙaura a ruƙunin daga gundumar Luweero a tsakiyar Uganda zuwa Yammacin Uganda. [1] [3]

A cikin shekarar 1985, sashin Nalweyiso ta ba da umarni, ta shiga cikin sojojin NRA da suka kai hari barikin sojoji na Mbarara. Bayan wannan turawa, Ƙungiyar Mata ta NRA ta zauna a Fort Portal, har sai da yakin ya ƙare a shekarar 1986. [1]

A shekarar 1986, lokacin da NRA ta kwace mulki, an baiwa Nalweyiso muƙamin kyaftin, kuma ta naɗa kwamandan reshen mata 800 na soja, a lokacin. Ta ci gaba da samun matsayi kuma a shekara ta 2000 ta kasance a matsayin Laftanar Kanal. [1] [3]

Sama da shekaru goma kafin kara mata girma zuwa Manjo Janar, ta yi aiki a gidan gwamnatin Uganda a matsayin mataimakinya da mai bawa shugaban Uganda shawara kan harkokin soji. [1] [3] [4]

A cikin watan Fabrairun 2019, a cikin wani atisayen gabatarwa wanda ya shafi maza da mata sama da 2,000 na UPDF, an kara mata girma daga muƙamin Major-General zuwa Laftanar-Janar. [5]

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin shekarar 1974, yayin da take farar hula, Nalweyiso ta auri wani hafsan soja. Daga baya ta rabu da mijinta. Ita ce mahaifiyar 'ya'ya huɗu. [1] [3]

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 1.5 1.6 1.7 1.8 Kato, Joshua (3 October 2011). "Home Life style Brig. Nalweyiso: Woman of many firsts". Retrieved 20 June 2017.
  2. Ankunda, Paddy (13 January 2017). "Nalweyiso promoted to Major General in new army reshuffle". Retrieved 20 June 2017.
  3. 3.0 3.1 3.2 3.3 3.4 3.5 3.6 3.7 Mulema, Najibu (13 January 2017). "Maj. Gen Proscovia Nalweyiso; The highest-ranking female officer in UPDF". Archived from the original on 14 January 2017. Retrieved 20 June 2017.
  4. Lubwama, Siraje (3 August 2016). "Uganda: Brig Nalweyiso Rallies Behind Gen Kayihura on Police Brutality". Retrieved 20 June 2017.
  5. Monitor Reporter (8 February 2019). "Museveni promotes over 2,000 UPDF Officers". Retrieved 8 February 2019.