Rahila Ruto
13 Satumba 2022 - | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | Kakamega (en) | ||
| ƙasa | Kenya | ||
| Ƴan uwa | |||
| Abokiyar zama | William Ruto | ||
| Karatu | |||
| Makaranta | Jami'ar Kenyatta licentiate (en) The Catholic University of Eastern Africa (en) | ||
| Harsuna | Turanci Harshen Swahili | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||
Rachel Chebet Ruto (an haife ta a ranar 20 ga watan Nuwamba 1969) malamar makaranta ce 'yar ƙasar Kenya, wacce a yanzu take aiki a matsayin Uwargidan Shugaban ƙasar Kenya. Ita ce matar William Ruto, Shugaban ƙasar Kenya na biyar kuma na yanzu.
Ilimi da aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Ta yi karatun firamare a Likuyani, gundumar Kakamega, sannan ta ci gaba zuwa Makarantar Sakandare ta 'Yan Mata ta Butere [1] da matakan O da A. Ta yi karatun digiri na farko, daga baya aka kira ta ta shiga Jami'ar Kenyatta, inda ta yi digiri na farko a fannin Ilimi (Fasaha). Ta ci gaba da karatun digiri na biyu a fannin Fasaha [2] a shekarar 2011 a Jami'ar Katolika ta Gabashin Afirka.
Duk da cewa ta karanci Ilimi, ba ta samu damar yin aikin koyarwa ba tsawon lokaci yayin da ta yi ritaya da son rai kuma ta shiga harkar kasuwanci a fannin yawon buɗe ido da tafiye-tafiye wanda ya mayar da hankali kan biranen da masu yawon buɗe ido ke taruwa a ƙasar.
Taimako da fafutuka
[gyara sashe | gyara masomin]Ta zama mai fafutukar kare haƙƙin mata da ƙarfafa su.
A ranar 17 ga watan Janairun 2014, an ba Rachel Ruto kyautar girmamawa ta duniya kan ƙarfafa mata a Jami'ar Binary da ke Malaysia.[3]
Ta daɗe tana fafutukar neman rayuwa mai kyau ta hanyar motsa jiki kamar hawa keke kuma ta ƙaddamar da Shirin Mama Keke a watan Satumba don haɓaka wannan aikin. [4]
A watan Maris a shekarar 2023, ta nuna adawa da dangantakar jinsi ɗaya, bayan hukuncin Kotun Koli ta Kenya, da ya bai wa ƙungiyoyin LGBTQ damar shiryawa.[5]
Iyali
[gyara sashe | gyara masomin]An yi auren Rachel da William a shekarar 1991 [6] a cocin AIC. Sun haɗu a lokacin da suke jami'a a wani taron ƙungiyar Kiristoci a Jami'ar Nairobi. Rachel tana karatun ilimi a Jami'ar Kenyatta yayin da mijinta ke karatun ilimin tsirrai da dabbobi a Jami'ar Nairobi. Ma'auratan suna da 'ya'ya shida ciki har da Charlene. Ma'auratan sun ɗauki jaririyar Nadia, wacce aka binne da rai. Sun sanya wa jaririn suna Cherono, bayan mahaifiyar Ruto. [7]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Nyanchwani, Silas. "Where Manduli, Rachel Ruto were among the best". Standard Entertainment and Lifestyle (in Turanci). Retrieved 2021-12-02.
- ↑ "DP William Ruto congratulates his wife Rachel after her graduation". The Standard (in Turanci). 2016-10-30.
- ↑ "Deputy President's Wife Rachel Ruto Gets Awarded With A Prestigious International Award". Ulizalinks.co.ke. 17 January 2014.
- ↑ Mabonga, Masolo (2020-12-20). "Rachel Ruto cycles for 146km to promote non-motorised mode of transport". Tuko.co.ke − Kenya news. (in Turanci). Archived from the original on 2021-06-24. Retrieved 2021-06-17.
- ↑ "Kenya's First Lady declares national prayers against homosexuality". Vanguard. Lagos, Nigeria. Retrieved 6 March 2023.
- ↑ "Rachel Ruto hosts Bishop who officiated wedding with Ruto". The Star (in Turanci). 2022-09-16. Retrieved 2022-09-22.
- ↑ "Rachel Ruto Biography, Age, Education, Family Career and Projects". The Informer whownskenya (in Turanci). 2022-09-22. Retrieved 2022-09-22.