Jump to content

Rahma MK

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Rahma MK

Ta kasance Jaruma ce a masana'antar fim din Hausa wato kanniwud, Ta shahara ne a sanadiyyar fim din da take a Tashar arewa 24 Mai suna KWANA CASA'IN, inda ta fito a matsayin matar gwamna hajiya Rabi bawa Mai kada.[1]

Takaitaccen Tarihin Ta

[gyara sashe | gyara masomin]

Rahama haifaffiyar garin Zaria ce dake jihar kaduna, tayi karatun firamare da sakandiri da islama a cikin garin Zaria. Ta fara fim tsawon shekaru 10 kenan, jarumar tayi aure inda tai aure a jihar filato Inda har Allah ya azurta ta da Yara biyu, SE auren nata ya mutu. Daga Nan ta shigo masana'antar fim dama tun tana karama take da burin fim , ta fara fim a shekarar 2013 inda ta fara da fim Mai suna kinci amanata, Sai fim din Nisan kiwo wadanda sune suka haskakata kafin kwana casa'in. Bayan fim jarumar tana aiki da hukumar ilimi a jihar kaduna sannan tana kasuwanci. Ta kuma yin wani auren a shekarar 2021 , a yanzu haka ta haifi diya mace.

Fina finan ta.

  • Kinci amanata[2]
  • Nisan kiwo
  • Biyayyar aure
  • Dillaliya
  • Mujin yayata
  • Da sauran su[3]
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-29. Retrieved 2023-07-29.
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-29. Retrieved 2023-07-29.
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-29. Retrieved 2023-07-29.