Jump to content

Ramadan Asswehly

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ramadan Asswehly
Rayuwa
Haihuwa Misrata (en) Fassara, 1879
ƙasa Tripolitanian Republic (en) Fassara
Mutuwa 1920
Ƴan uwa
Yara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da nationalist (en) Fassara
Aikin soja
Ya faɗaci Sirte revolt (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci

Ramadan Sewehli, also spelled as Ramadan al-Suwayhili, [1] Ramaḍān al-Swīḥlī (c. 1879 – 1920) ya kasance fitaccen ɗan kishin ƙasa na Tripolitaniya a farkon mamayar Italiya a shekarar 1911 kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa Jamhuriyar Tripolitaniya. [1]

Ya yi yaƙi da Daular Usmaniyya da Italiya a lokacin Yaƙin Italo-Turkiyya, amma bayan kammala yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 1912, ya jagoranci tawaye ga ruƙunin Italiya a Sirte. Da ɓarkewar yakin duniya na ɗaya, Italiyawa sun janye daga Misrata.[2] Ganin wannan fa'ida, daga baya ya shiga yakin Gasr Bu Hadi da Italiya. Shekaru da dama, ya yi nasarar karfafa garin Misrata a matsayin mafaka ga dakarun Ottoman da gundumar siyasa mai cin gashin kanta. A cikin shekarar 1916, sojojinsa sun yi arangama da sojojin Senussi da aka aika zuwa Sirte don karɓar haraji daga jama'ar yankin.[3] Kakan Abdulrahman Sewehli ne.

  1. 1.0 1.1 Tastekin, Fehim (2019). "Are Libyan Turks Ankara's Trojan horse?". Al-Monitor. Retrieved 15 September 2019.
  2. St John, Ronald Bruce (4 June 2014). Historical Dictionary of Libya. Rowman & Littlefield. p. 316. ISBN 9780810878761.
  3. St John, Ronald Bruce (4 June 2014). Historical Dictionary of Libya. Rowman & Littlefield. p. 316. ISBN 9780810878761.