Jump to content

Raquel Ilombé

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Raquel Ilombé
An haife shi Raquel del Pozo Epita1938 Corisco, Guinea ta Spain

Guinea ta Mutanen Espanya
Ya mutu 1992 (shekaru 53-54) Madrid, Spain 
Sunan alkalami Raquel Ilombé
Aiki Mawallafi, marubucin
Harshe Mutanen Espanya
Ƙasar Mutanen Espanya, Equatorial Guinea
Ilimi Cibiyar Conservatory ta Madrid

Raquel del Pozo Epita (1938-1992), wanda aka fi sani da Raquel Ilombé, mawaki ne kuma marubucin na Equatorial Guinea, wacce ta rubuta a harshen Mutanen Espanya.[1][2]

Tarihi da farkon rayuwarsa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife ta ne a Guinea ta Mutanen Espanya (a yau Equatorial Guinea), a tsibirin Corisco, ga uwa 'yar Equatorial Guinean da uba mutumin Sifaniya. A lokacin yarintar ta, ta koma Burgos, Spain. Ta karanci kiɗa da waka a makarantar Conservatory ta Madrid . Ta koma Equatorial Guinea ne kawai daga baya a rayuwa bayan ta yi aure, kuma ta yi tafiye-tafiye da yawa ba tare da cikas ba a lokacin Francisco Macías Nguema . Ta mutu a Madrid a shekarar 1992.[2]

Waƙoƙi da rubuce-rubuce

[gyara sashe | gyara masomin]

An san Ilombé "a matsayin mace ta farko da ta fara buga littafi a Equatorial Guinean". Sunan ta ya samo asali ne daga ɗayan manyan haruffa huɗu na tatsuniyar Ndowe. A cikin wannan al'adar baki, "Ilombe" suna ne na wata yarinya mai biyayya.[3]

Aikinta na farko da aka fara wallafawa shine Ceiba, tarin wakokin shayari da aka wallafa a cikin shekara ta 1978.[1] Daya daga cikin muhimman batutuwan ta na soyayya ne. Ilombé ta rubuta shayarai a tsakanin 1970 zuwa 1977 kuma an zayyano su ne a jere. Ana iya ganin nazari tsakanin al'adun gargajiya ta Afurka da Katolika a cikin su, kamar a cikin "Quién Soy" (Hausa: "Wanene ni"). A yayinda nazarin ta a kan abubuwan da ke zahiri sun ta'allaka ne a kan kasar Sufaniya da Equatorial Guinea, ayyukanta basu shafi rayuwar ta a sauran kasashen waje ba. Ana kiran jerin wakokinta da suna Bishiyar Ceiba pentandra, Bishiyar kasar Equatorial Guinea wanda ke jikin tutar kasan; ana daukan bishiyar a matsayin abu mai tsarki.[2]

A cikin shekarar 1988, ta wallafa Leyendas Guineanas (Hausa: Shahararrun Guinean), tarin labarai daga shahararrun kasar Guinea guda takwas na daga kabilu kasar; Fang, Bubi, da kuma Ndowe. Ana daukan shi littafin yara na farko na kasar Equatorial Guinea. Don samun bayanan da ta saka a cikin littafin, hakan ya sa tayi yawo a kauyuka masu nisa a Equatorial Guinea, don nemo al'adu kasar Guinea da suke bacewa.[2][4]

Ta kuma wallafa wakokin shayari irin su "Nerea", "Ausencia", da kuma "Amor", kuma ta rubuta wakar "Olvido" amma bata wallafa shi ba.[5]

  1. 1 2 "Ilonbé, Raquel (Equatorial Guinea)". Literary Map of Africa. Ohio State University Libraries. 2010. Retrieved 2016-10-16.
  2. 1 2 3 4 "Raquel Ilonbe". asodegue.org (in Spanish). Archived from the original on 2020-10-07. Retrieved 2016-10-16.CS1 maint: unrecognized language (link)
  3. "Los ríos hablan, de Raquel Ilonbé". Versovia.com (in Spanish). 2014-11-23. Retrieved 2016-10-16.CS1 maint: unrecognized language (link)
  4. "Leyendas Guineanas" (in Spanish). Libros Tobal. Retrieved 2016-10-16.CS1 maint: unrecognized language (link)[permanent dead link]
  5. "Raquel Ilonbe". asodegue.org (in Spanish). Retrieved 16 October 2016.