Jump to content

Redfoo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Redfoo
Rayuwa
Cikakken suna Stephen Kendal Gordy
Haihuwa Los Angeles, 3 Satumba 1975 (50 shekaru)
ƙasa Tarayyar Amurka
Harshen uwa Turanci
Ƴan uwa
Mahaifi Berry Gordy
Ahali Rockwell (en) Fassara, Kerry Gordy (en) Fassara da Rhonda Ross Kendrick (en) Fassara
Ƴan uwa
Yare Gordy family (en) Fassara
Karatu
Makaranta Palisades Charter High School (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a mawaƙi, rapper (en) Fassara, mai rubuta waka, mai tsara, disc jockey (en) Fassara, mai rawa, mai gabatarwa a talabijin, jarumi, tennis player (en) Fassara da investor (en) Fassara
Tennis
 
Mamba LMFAO (en) Fassara
Sunan mahaifi Redfoo, Red Foo da Kendal
Artistic movement pop rap (en) Fassara
hip house (en) Fassara
electronic dance music (en) Fassara
electropop (en) Fassara
Kayan kida murya
piano (en) Fassara
keytar (en) Fassara
Jadawalin Kiɗa Interscope Records (mul) Fassara
Cherrytree Records (en) Fassara
will.i.am Music Group (en) Fassara
IMDb nm0330713
redfoo.com
Redfoo
Redfoo a shekarar 2011.
Redfoo a shekarar 2011.
Background information
Sunan haihuwa Stefan Kendal Gordy
Born (1975-09-03) Satumba 3, 1975 (shekaru 50)
Los Angeles, California, Amurka
Origin Amurka
Genre (en) Fassara Hip hop, rap, EDM, house, pop, dance
Mawaƙi, mai shirya waƙa, ɗan rawa, DJ
Kayan kida Murya, keytar, ganga, piano, guitar, synthesizer
Years active 1993–zuwa yau
Record label (en) Fassara Party Rock, Will.i.am Music, Cherrytree, Interscope, Bubonic
Associated acts LMFAO, RFDK

Stefan Kendal Gordy (an haife shi a ranar 3 ga watan Satumba, 1975), wanda aka fi sani da sunan sa na dandalin waka Redfoo, mawaƙin Amurka ne, mai shirya waƙoƙi, ɗan rawa, kuma DJ.

A shekarar 2006, ya kafa ƙungiyar LMFAO tare da ɗan uwansa SkyBlu (Skyler Austen Gordy). Sun saki faya-fayai guda biyu kafin su rabu a shekarar 2012.[1] Shi ne ɗan ƙarami ga wanda ya kafa Motown Records, wato Berry Gordy.[2]

Mujallar "Focus On" ta sanya Redfoo a cikin jerin mawaƙan dance 100 da suka fi shahara a tarihin Amurka.[3]

Tarihin rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Redfoo a ranar 3 ga Satumba, 1975, ga Berry Gordy, wanda ya kafa kamfanin Motown, da kuma Nancy Leiviska. Ya yi makarantar sakandare tare da will.i.am da GoonRock. Ya kammala karatunsa a Palisades Charter High School a Los Angeles a 1995.

Aikin waƙarsa ya samu tasiri sosai daga mahaifinsa da mahaifiyarsa. Tun yana yaro yana yawan zuwa kallo a wurin wasannin manyan mawaƙa. A fagen waƙa, waɗanda suka fi burge shi su ne Michael Jackson da Diana Ross. Duk da kasuwancin iyalinsa, abin da ya fi ba wa muhimmanci shi ne wasan tennis, amma da ya ji rauni a hannunsa, ya fara ɗaukar waƙa da muhimmanci tun yana ɗan shekara 16.

Ya shiga gasar US Open a 2012 da Australian Open a 2013. Ya fara soyayya da 'yar wasan tennis Viktoria Azarenka a 2012, amma sun rabu a 2014. Yana da kamfanin tufafi na Party Rock kuma yana daukar nauyin gasar Party Rock Open.

Sana'ar Waƙa

[gyara sashe | gyara masomin]

1993-2005: Farkon farawa da Balance Beam

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 1993, Redfoo ya shirya waƙar "Back in the Day" don mawaƙi Ahmad, wacce ta samu kyautar zinare daga RIAA a shekarar 1994.[4] A shekarar 1996 ya kulla yarjejeniya da Bubanic Records kuma ya yi aiki tare da Dre' Kroom a kundi na farko mai suna Balance Beam, wanda aka saki a ranar 28 ga Oktoba, 1997.[5] A shekarar 1998, ya yi aiki a waƙar Duet ta The Black Eyed Peas.[6]

2006-2012: LMFAO

[gyara sashe | gyara masomin]

Redfoo ya kafa ƙungiyar electropop LMFAO da ɗan uwansa SkyBlu a 2006. Bayan sun yi waƙoƙin gwaji, will.i.am ya haɗa su da shugaban Interscope Jimmy Iovine. Suka saki kundi na farko Party Rock a ranar 7 ga Yuli, 2009. Waƙarsu ta farko I'm in Miami Bitch ta samu karɓuwa sosai. A shekarar 2011, sun saki "Party Rock Anthem" wacce ta zama waƙarsu mafi shahara a duniya, ta sayar da kofi sama da miliyan 10 a Amurka kawai. Daga baya suka saki waƙoƙi kamar "Champagne Showers" da "Sexy and I Know It". A ranar 21 ga Satumba, 2012, LMFAO sun ba da sanarwar rabuwa don mayar da hankali kan ayyukan kansu.

2012-2016: Aikin shi kaɗai

[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Disamba na 2012, Redfoo ya saki waƙarsa ta farko "Bring Out the Bottles". A 2013 ya saki "Let's Get Ridiculous", wacce ta kai lamba daya a Ostiraliya. Ya kasance alƙali a gasar The X Factor a Ostiraliya a 2013. A shekarar 2014, ya saki "New Thang", wacce ta samu farin jini sosai har a TikTok a 2020. Ya kuma saki kundi na Party Rock Mansion a 2016.

2017-zuwa yau: Hutun waƙa

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan kundi na Party Rock Mansion, Redfoo ya saki "Brand New Day" a 2017 da "Everything I Need" a 2018. A shekarar 2023, bayan hutun shekaru biyar, ya saki sabuwar waƙa mai suna "Long Live Party Rock".

Kundin Waƙoƙi (Albums)

[gyara sashe | gyara masomin]
Suna Bayani
Ahmad (A matsayin mai shirya waƙa)
  • Shekara: 1994
  • Kamfani: Bubonic Records
Balance Beam
  • Shekara: 1997
  • Kamfani: Bulbonic Records
Party Rock (LMFAO)
  • Shekara: 2009
  • Kamfani: Interscope
Sorry for Party Rocking (LMFAO)
  • Shekara: 2011
  • Kamfani: Interscope
Party Rock Mansion
  • Shekara: 2016
  • Kamfani: Party Rock Records

Fina-finai da Talabijin

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Very Heavy Love (2001)
  • Potheads: The Movie (2006)
  • Last Vegas (2013)
  • Alvin and the Chipmunks: The Road Chip (2015)
  • Tattooed Love (2015)
  • Deported (2020)
  • David's Vlog – shirin talabijin (2016)

Waƙoƙin Fina-finai

[gyara sashe | gyara masomin]

Wasu daga cikin fina-finan da aka yi amfani da waƙoƙin sa:

  • Step Up 3D (2010) da waƙar Shooting Star
  • Project X (2012) da waƙar Outta Your Mind
  • 21 Jump Street (2012) da waƙar Party Rock Anthem
  • American Reunion (2012) da waƙar Sexy and I Know It
  • Hotel Transylvania (2012) da waƙar Sexy and I Know It
  • Last Vegas (2013) da waƙar Party Rock Anthem
  1. "LMFAO 2006".
  2. "LMFAO Berry Gordy Father AMAs".
  3. "Ahmad album Redfoo".
  4. "RIAA Gold Platinum".
  5. "Balance Beam".
  6. "Duet".

Ma