Rejoice Timire
ga Augusta, 2018 - | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa |
Mberengwa District (en) | ||
| ƙasa | Zimbabwe | ||
| Mutuwa | 11 ga Augusta, 2021 | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||
| Wurin aiki | ZANU-PF | ||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa | ZANU-PF | ||
Rejoice Timire (7 Afrilu 1959 - 11 ga Agusta 2021) 'yar gwagwarmayar kare hakkin naƙasassu ta Zimbabwe ce kuma 'yar siyasa wacce ta yi aiki a Majalisar Dattawan Zimbabwe daga shekarun 2018 har zuwa mutuwarta a shekarar 2021, wacce ke wakiltar mazaɓar naƙasassu ta musamman. Ta daɗe a matsayin mai fafutukar kare hakkin naƙasassu, ta taka muhimmiyar rawa wajen kara manufofin naƙasassu a cikin Kundin Tsarin Mulki na Zimbabwe.
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Rejoice Timire a ranar 7 ga watan Afrilu 1959 a ƙauyen Musume a gundumar Mberengwa, Zimbabwe. Ta halarci makarantar firamare ta Matedzi da kuma Sakandaren Musume. Ta yi karatun kasuwanci a jami'a, kuma ta zama 'yar kasuwa a tsakiyar shekarun 1990. A cikin shekarar 1998, Timire ta yi hatsari a Cape Town, Afirka ta Kudu, wanda ya haifar da mummunan rauni na kashin baya kuma ta buƙaci ta yi amfani da keken guragu. Bayan hatsarin da ta yi, ta zama fitacciyar mai ba da shawara ga naƙasassu, musamman mata naƙasassu, a Zimbabwe. [1] Ta zama mamba a kungiyar tallafawa mata naƙasassu a shekarar 2003, kuma ta zama babbar darektar kungiyar a shekarun 2010. [2] [3] Ta kasance mamba a kwamitin gudanarwa na kungiyar mata ta Zimbabwe da hukumar naƙasassu. [1]
A watan Agustan 2018, an zaɓi Timire a matsayin 'yar majalisar dattawan ƙasar Zimbabwe domin ta wakilci naƙasassu, mazaɓar da aka keɓe na musamman inda ake zaɓen sanata ɗaya da mace ɗaya daga wata kwalejin zaɓe da aka buɗe ga wakilai daga kungiyoyin naƙasassu masu rijista. Ta zauna a matsayin mamba a jam'iyyar ZANU-PF mai mulki. Kafin ta zama sanata, ta kasance mai ba da shawara ga wani shiri na haɗin gwiwa da Tarayyar Turai da Majalisar Ɗinkin Duniya suka yi game da cin zarafin mata masu naƙasa a Zimbabwe. [1] [2]
A matsayinta na sanata, Timire ta haɗa hannu da Majalisar Ɗinkin Duniya Haɗin Kan 'Yancin Naƙasassu da sauran ƙungiyoyin kare haƙƙin naƙasassu don tsara manufar naƙasassu a hukumance ga Zimbabwe. Wannan tsari an yi niyya ne don sabunta Dokar Naƙasassu da ta gabata ta shekarar 1992 da kuma ɗaure ta da Kundin Tsarin Mulki na Zimbabwe. Shugaba Emmerson Mnangagwa ne ya kaddamar da manufar naƙasassu ta ƙasa a hukumance a watan Yuni 2021. [2] [4] Timire ta kuma ba da shawarar samun ingantacciyar hanyar zubar da ciki, yana mai yin nuni da ktaruwar mace-mace daga zubar da ciki ba bisa ka'ida ba, da kuma ƙara yawan albarkatun kula da lafiyar kwakwalwa ga naƙasassu yayin bala'in COVID-19. [5] [6] A watan Mayun 2021, ta kaɗa kuri'ar amincewa da yiwa kundin tsarin mulki kwaskwarima wanda ya faɗaɗa ikon shugaba Mnangagwa. [7]
Timire ta mutu daga cutar COVID-19 a Asibitin Mbuya Dorcas da ke Harare a ranar 11 ga watan Agusta 2021, yana da shekaru 62. An binne ta a makabartar Glenforest ta Harare. Wasu fitattun masu fafutuka na naƙasassu da dama da suka haɗa da shugabannin hukumar kula da naƙasassu ta ƙasa da kuma Deaf Zimbabwe Trust, da kuma wasu naƙasassu sanata Watson Khupe sun yaba da rasuwarta. [1] [8]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- 1 2 3 4 "Senator Rejoice Timire Dies". The Zimbabwe Mail (in Turanci). 2021-08-11. Archived from the original on 2023-11-18. Retrieved 2023-11-18.
- 1 2 3 "Addressing Inequalities in Parliament - Senator Rejoice Timire". United Nations Development Programme (in Turanci). June 28, 2019. Retrieved 2023-11-18.
- ↑ Gama, Mavis (2016-10-03). "Abaphila Lobugoga Bakhala Ngemithetho Engelancedo" [Those Who Live in Old Age Complain About Unhelpful Laws]. Voice of America (in North Ndebele). Retrieved 2023-11-18.
- ↑ Machivenyika, Farirai (June 12, 2021). "People Living With Disabilities Hail New Policy". The Herald (in Turanci). Archived from the original on 2024-12-17. Retrieved 2023-11-18.
- ↑ Chikono, Melody (December 18, 2019). "Zimbabwe's High Maternal Mortality Rate Could Push a Lift on Abortion Restrictions". Women's Media Center (in Turanci). Retrieved 2023-11-18.
- ↑ "Govt Calls for End to Mental Health Stigma". The Street Journal (in Turanci). 2020-10-15. Archived from the original on 2023-11-18. Retrieved 2023-11-18.
- ↑ Mangwaya, Miriam (2021-05-05). "'Sad Day for Democracy'". Nehanda Radio (in Turanci). Retrieved 2023-11-18.
- ↑ Njema, Safari (2021-08-12). "Seneta Rejoice Timire, Avo Vakashaya neChirwere cheCovid-19, Varadzikwa Nhasi muHarare" [Senator Rejoice Timire, Who Died of Covid-19, Was Laid to Rest Today in Harare]. Voice of America (in Shona). Retrieved 2023-11-18.