Jump to content

Rikicin Fatah-Hamas

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentRikicin Fatah-Hamas

Iri rikici
Bangare na Rikicin siyasar Falasdinu
Kwanan watan 25 ga Janairu, 2006
Wuri Zirin Gaza

Rikicin Fatah da Hamas dai wani rikici ne da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin kungiyar Fatah da ke gabar yammacin kogin Jordan da kuma ƙungiyar Hamas dake zirin Gaza . Rikicin ya fara ne bayan Intifada ta biyu saboda Fatah ta yi jayayya cewa Hamas ta lashe zaɓen 2006 a Hukumar Falasɗinawa ta PNA. Ya ƙara girma lokacin da Hamas ta karɓe iko da yankin Gaza da karfin soja a shekara ta 2007 a lokacin yakin Gaza . Ƙungiyoyin biyu sun yi kokarin sasantawa a cikin 'yan shekarun nan kuma tun daga lokacin sun sami kansu a gefe guda a yakin Isra'ila da Hamas na 2023.[1]

  1. "Over 600 Palestinians killed in internal clashes since 2006". Ynetnews. Ynetnews.com. June 20, 1995. Archived from the original on July 4, 2011. Retrieved April 24, 2011.