Jump to content

Ringim

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ringim


Wuri
Map
 12°17′00″N 9°28′00″E / 12.2833°N 9.4667°E / 12.2833; 9.4667
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar Jigawa
Yawan mutane
Faɗi 192,024 (2006)
• Yawan mutane 181.67 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 1,057 km²
Altitude (en) Fassara 387 m
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 733
Kasancewa a yanki na lokaci

Ringim karamar hukuma ce dake a Jihar Jigawa, Arewa maso yamman Nijeriya.

Yarima Adnan da Yarima Ajman, na Ringim

Ringim karamar hukuma ce (LGA) a jihar Jigawa, Najeriya. Hedkwatarta tana cikin garin Ringim, LGA tana da yanki mai girman kilomita 1,057 kuma tana da yawan jama'a 192,024 a ƙidayar 2006.[1] Masarautar Ringim ta fara aiki ne a watan Nuwamba, 1991, sakamakon kirkiro jihar Jigawa daga jihar Kano a ranar 27 ga watan Agustan 1991 da shugaban kasa kuma babban kwamandan[2] sojojin Najeriya na lokacin, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi. Masarautar ta kunshi kananan hukumomi hudu, wato: Ringim, Taura, Garki da Babura. Mai Martaba Sarkin Ringim na yanzu, HRH Alh. (Dr) Sayyadi mahmoud usman (CON) shine sarkin fulani na daya na Ringim. Sarkin ya kasance shugaban kungiyar hadin kan kasashen yammacin Afirka.[3]

Cigaban ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Shekara 1930 shine farkon ci gaban ilimi daban-daban a Ringim. A shekarar 1930 aka kafa makarantar firamare ta farko a garin Ringim (Katutu Primary School). Daliban da aka dauka a shekarar 1931 sun kai 39. A 1954, an kafa wata makarantar firamare (Sabon Gida Senior. Primary School). Sakamakon shirin UPE a shekarar 1976 an kara gina wasu makarantu a garin Ringim sannan daliban sun karu, makarantar firamare ta Galadanchi da mayar da St.Peters zuwa makarantar firamare ta Sabon Gari. Wannan ya sanya adadin makarantun firamare a Ringim ya koma hudu baya ga wasu Makarantun Islamiyya. A shekarar 9176 aka koma makarantar sakandiren gwamnati zuwa Ringim bayan ta zauna na dan lokaci na tsawon shekaru biyu a dawakin Tofa sannan aka kafa babbar jami’a a karkashin Polytechnic Jigawa a shekarar 1991.

Ƙaramar hukumar Ringim tanada mazaɓu guda goma (10).

 • Chai-chai
 • Dabi
 • Kafin Babushe
 • Karshi
 • Kyarama
 • Ringim
 • Sankara
 • Sintilmawa[4]
 • Tofa
 • Yandutse
 1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-02-13. Retrieved 2022-03-21.
 2. https://www.vanguardngr.com/2012/01/why-ringim-was-sacked/
 3. https://dailytrust.com/amp/emir-of-ringim-a-dignified-silver-jubilee
 4. https://www.manpower.com.ng/places/wards-in-lga/379/ringim