Rosebud Kurwijila
| Rayuwa | |
|---|---|
| ƙasa | Tanzaniya |
| Harshen uwa | Harshen Swahili |
| Karatu | |
| Makaranta |
University of London (en) University of East Anglia (mul) Sokoine University of Agriculture |
| Harsuna |
Turanci Harshen Swahili |
| Sana'a | |
| Sana'a | ɗan siyasa |
Rosebud Violet Kurwijila, 'yar ƙasar Tanzaniya, ita ce Kwamishiniyar Tattalin Arzikin Karkara da Noma ta Tarayyar Afirka. Ta kasance mai kula da ci gaban shirye-shirye na ACTIONAID a ƙasar Tanzaniya.
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Ta yi digirin farko a fannin aikin gona daga Jami’ar Aikin Gona ta Sokoine, Tanzania (1976), Digiri na biyu a fannin Tattalin Arziki na Aikin Noma daga Jami’ar London (1983) da kuma masters a Falsafa a fannin tattalin arziki daga Jami’ar Gabashin Anglia (1994).
A lokacin aikinta, ta yi aiki a lokuta da dama a matsayin mai ba da shawara a fannoni daban-daban da suka shafi Noma, Tattalin Arzikin Karkara da Tsaron Abinci. Daga shekarun 1995 - 1997, ta kasance babbar mai ba da shawara a wani kamfani mai ba da shawara inda ta magance ayyukan saye da aiwatar da ayyukan.
Ta buga kasidu da dama a cikin mujallun ƙasa da ƙasa kan batun samar da abinci, tattalin arzikin karkara, fasahar noma da sauran batutuwa masu alaka.
Fannin iya aikinta sun haɗa da sarrafa shirye-shirye, tsara manufofi da kuma kula da ma'aikata.
Tana da 'ya'ya huɗu. Mijinta, Farfesa Lusato Kurwijila, ya rasu a Morogoro, Tanzania a ranar 8 ga watan Agusta 2021. [1]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Archived copy". Archived from the original on 2011-09-27. Retrieved 2008-11-22.CS1 maint: archived copy as title (link)