Saeed Gul
| Rayuwa | |
|---|---|
| Sana'a | |
| Sana'a | ɗan siyasa |
| Imani | |
| Jam'iyar siyasa |
Jamiat Ulema-e-Islam (en) |
Saeed Gul ɗan siyasan Pakistan ne wanda ya taɓa zama memba a majalisar lardin Khyber Pakhtunkhwa, daga watan Mayun shekarar 2013 zuwa Mayun shekara ta 2018. A baya ya kasance memba na majalisar lardin Khyber Pakhtunkhwa daga shekarar 2002 zuwa 2007.
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Yana da digiri na Master of Arts.[1]
Sana'ar siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]An zaɓe shi ɗan majalisar dokokin lardin arewa maso yamma a matsayin ɗan takarar Muttahida Majlis-e-Amal daga mazaɓar PF-96 (Lower Dir-III) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2002. Ya samu ƙuri'u 10,326 sannan ya doke Ɗan takarar jam'iyyar Pakistan Peoples Party (PPP). [2]
An sake zaɓe shi a Majalisar lardin Khyber Pakhtunkhwa a matsayin ɗan takarar Jamaat-e-Islami Pakistan daga Mazaɓar PK-96 (Lower Dir-III) a babban zaɓen Pakistan na 2013 . Ya samu ƙuri'u 14,193 sannan ya doke dan takarar jam'iyyar PPP. [3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Profile". www.pakp.gov.pk. KP Assembly. Archived from the original on 7 June 2017. Retrieved 15 January 2018.
- ↑ "2002 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 26 January 2018. Retrieved 30 April 2018.
- ↑ "2013 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 1 February 2018. Retrieved 29 April 2018.