Jump to content

Safia Juuko Nalule

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Safia Juuko Nalule
Member of Parliament of Uganda (en) Fassara

Rayuwa
HaihuwaUganda, 15 ga Maris, 1966 (60 shekaru)
ƙasaUganda
Karatu
MakarantaJami'ar Makerere
HarsunaTuranci
Sana'a
Sana'adisability rights activist (en) Fassara, ɗan siyasa da legislator (en) Fassara

Safia Juuko Nalule (an haife ta a ranar 15 ga watan Maris 1966 [1] ) 'yar gwagwarmayar kare haƙƙin naƙasassu ce 'yar ƙasar Uganda, 'yar siyasa kuma 'yar majalisa wacce ta kasance zaɓaɓɓiyar wakiliyar mata ga Naƙasassu, Yankin Tsakiyar, Uganda a Majalisar Dokokin Uganda ta goma. [2] A watan Afrilun 2021, an naɗa ta shugabar Hukumar Samar da Dama na Daidaito ta Uganda (EOC). [3] A siyasance, tana da alaƙa da jam'iyyar National Resistance Movement [4] a ƙarƙashin tikitin da ta tsaya takara a babban zaɓe na shekarar 2016. [2]

Tarihi da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

A cewar yanar gizon gidan Hukumar Daidaita Dama, An haifi Nalule a Mawokota, gundumar Mpigi ɗiya ce ga marigayi Mista Lule Moses da Mrs. Nanyonga Jane Lule. [5]

Nalule ta sami digiri na farko daga Jami'ar Makerere a shekarar 1990 sannan kuma ta sami Takaddun shaida a Koyarwa a fannin Gudanar da Kasuwanci daga Kungiyar Kwadago ta Duniya a Tarayyar Ma'aikatan Uganda a shekarar 1991. A cikin shekarar 1996, ta sami takaddun shaida guda biyu Takaddun shaida a Jagoranci ga Mata daga ESAMI da Takaddun Jagoranci da Gudanar da Microfinance daga Mobility International USA (MIUSA). Ta biyo bayan haka ta sami Difloma a fannin Shari'a daga Cibiyar Bunƙasa Shari'a a shekarar 2006 sannan kuma ta samu Jagorar Fasaha a Hakkokin Ɗan Adam daga Jami'ar Makerere a shekarar 2016. [1]

Nalule ta kasance 'yar majalisa ce tun shekara ta 2006, tana zama a majalisar dokoki ta takwas da ta tara na Uganda. Tun daga shekarar 2020, an naɗa ta kwamishiniya a Hukumar Majalisa. [6] [7]

Kafin wannan lokacin, tsakanin shekarun 2005 zuwa 2006, ta yi aiki a matsayin kwamishiniya a hukumar nazarin tsarin mulki a ƙarƙashin ma'aikatar shari'a da tsarin mulkin Uganda. Ta kuma kasance kansila a majalisar birnin Kampala a lokacin tsakanin shekarun 1997 zuwa 2006. Daga shekarun 1996 zuwa 2005, ta yi aiki a matsayin Babbar Darakta na Cibiyar Sadarwar Mata da Naƙasassu da Resource Organisation a Uganda (DWNRO).

Ta yi aiki a matsayin mamba a kwamitin gudanarwa a kungiyar naƙasassu ta Uganda (NUDIPU) daga shekarun 2015 zuwa yau, da kuma kungiyar mata ta Uganda (UWONET) tsakanin shekarun 1990 zuwa 1997.

A shekarar 2017, ta kasance shugabar kwamitin kare hakkin ɗan Adam. [8] A matsayinta tna mace 'yar majalisa a majalisar dokoki ta goma ta Uganda, ta kasance memba na Ƙungiyar 'Yan Majalisun Mata ta Uganda (UWOPA) [9] da kuma mataimakiyar shugabar kwamitin naɗi. An saka ta a matsayin mamba a kwamitin kula da al'amuran al'ummar gabashin Afirka . [1]

  1. 1 2 3 "Nalule Juuko Safia". Parliament of Uganda. Retrieved 17 April 2020.
  2. 1 2 Electoral Commission (13 April 2016). "General Parliamentary Elections 2016 Gazette List" (PDF). Electoral Commission of Uganda. Retrieved 17 April 2020.
  3. "Sylvia Ntambi dropped as Museveni names Safia Nalule as new EOC Boss". Daily Express News (in Turanci). 2021-04-16. Retrieved 2022-02-25.
  4. National Resistance Movement (1 January 2017). "NRM Parliamentary Caucus". National Resistance Movement. Archived from the original on 4 October 2015. Retrieved 17 April 2020.
  5. "MESSAGE FROM THE CHAIRPERSON | EOC -UGANDA". THE EQUAL OPPORTUNITIES COMMISSION - EOC (in Turanci). Archived from the original on 2022-03-19. Retrieved 2022-02-25.
  6. "Parliamentary Commission". Parliament of the Republic of Uganda. 27 February 2018. Retrieved 17 April 2020.
  7. "Parliament Gets Two New Backbench Commissioners". Uganda Radio Network. Retrieved 17 April 2020.
  8. "The Human Rights Committee of Parliament meets the Equal Opportunities Commission (EOC) over recommendations made in the 18th Report of the Uganda Human Rights Commission (UHRC)". Equal Opportunities Commission. 10 May 2017. Archived from the original on 28 February 2021. Retrieved 17 April 2020.
  9. "Members of UWOPA of 10th Parliament". Uganda Women Parliament Association. Archived from the original on 18 April 2021. Retrieved 17 April 2020.