Jump to content

Sahaba el-Rehmania

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Sahaba el-Rehmania (Larabci: صحابة الرحمانية; m. c. 1528 / 934–5 AH) matar sarkin ƙasar Morocco na daular Sadiya Mohammed al-Shaykh kuma mahaifiyar Abu Marwan Abd al-Malik. Kasancewar ta samu hazaƙa a fannin diflomasiyya, ta rike mukamin jagorar siyasa a tsawon rayuwarta. Ta kasance jakadiya a daular Usmaniyya a kotun Sultan Murad III.

Tarihin rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Sahaba ta fito daga ƙabilar Rahamna, kabilar Hassan[1] Kabilarta tana da alaƙa da Sadiyawa kuma, a cikin shekarar alif 1525, sun shiga cikin harin da aka kai wa sansanin ƙasar Fotugal na Santa Cruz, a Agadir[2]. Ta auri Mohammed al-Shaykh a shekara ta 1528.

  1. "Chevauchées sahariennes". Le 360 Français (in French). Retrieved 2023-04-22.
  2. Pascon, Paul (1983). Le Haouz de Marrakech (in French). Centre universitaire de la recherche scientifique. p. 190. Retrieved 2023-04-23..