Sahabzada Yaqub Khan
Sahabzada Mohammad Yaqub Ali Khan 23 ga watan Disamba shekara ta 1920 - 26 ga watan Janairu shekara ta da alif dubu biyu da sha shidda 2016) ya kasance babban ɗan siyasan kasar Pakistan, diflomasiyya, soja, masanin harshe, kuma janar ne mai ritaya a cikin Sojojin kasar Pakistan.
Bayan raba kasar Indiya a shekara ta 1947, ya zaɓi kasar Pakistan kuma ya shiga aiki Sojo a kasar Pakistan inda ya shiga yakin Indo-Pakistan a shekara ta 1965. Ya kasance kwamandan rundunar sojin Gabas a Gabashin kasar Pakistan. An nada shi a matsayin gwamnan Gabashin kasar Pakistan a shekarar 1969 zuwa shekara ta 1971 amma ya dawo kasar Pakistan bayan ya gabatar da murabus dinsa a cikin tashin hankali. A shekara ta 1973, ya shiga aikin kasashen waje kuma an nada shi a matsayin Jakadan kasar Pakistan a kasar Amurka kuma daga baya ya hau matsayin ministan harkokin waje, yana aiki a karkashin Shugaba Zia-ul-Haq a shekarar 1982.
A matsayin sa na ministan harkokin waje ya taka muhimmiyar rawa a cikin Soviet an Afghanistan a shekarar ta (1979 zuwa 89) kuma ya shiga cikin tattaunawar kawo karshen Contras a Nicaragua shekara tav(1981 zuwa 87) a madadin Majalisar Dinkin Duniya. A cikin shekarun 1990s, ya yi aiki a matsayin jami'in Majalisar Dinkin Duniya na Yammacin Sahara har sai an sake nada shi a matsayin ministan harkokin waje a karkashin Firayim Minista Benazir Bhutto . Bayan ya yi ritaya daga ayyukan diflomasiyya a shekarar 1997, ya shafe sauran shekarunsa an Islamabad kuma ya mutu a Islama Bad a shekarar ta alif dubu biyu da goma sha shidda 2016.
An haifi Mohammad Yaqub Ali Khan a cikin manyan mutanen kasar Indiya a cikin reshen Rohilla na dangin Pashtun na Kheshgi a Rampur, lardunan United, Daular Indiya ta kasar Burtaniya a ranar 23 ga watan Disamba shekara ta 1920. Ya kuma kasance dangi na kusa da dangin Nawabs na Kasur, na Punjab.[1] Mahaifinsa, Sir Abdus Samad Khan ya kasance dan majalisa kuma ɗan siyasa wanda ya yi aiki a matsayin babban ministan Rampur, kuma a matsayin wakilin kasar Indiya da kasar Burtaniya a cikin League of Nations .
- ↑ "Fauzia Kasuri disclosure". Twitter.