Saleh Meki
1997 - 2009 ← Sebhat Ephrem - Amna Nurhusein (en) | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | 1948 | ||
| ƙasa | Tarayyar Amurka Eritrea | ||
| Mutuwa | Asmara, 2 Oktoba 2009 | ||
| Yanayin mutuwa | Sababi na ainihi (Ciwon zuciya) | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa | People's Front for Democracy and Justice (en) | ||
Saleh Meki (1948 - Oktoba 2, 2009) ɗan siyasan Eritrea ne kuma ministan gwamnati. Ya kasance memba na kungiyar 'yantar da jama'ar Eritrea, wacce ke da ofisoshi a yankin San Francisco Bay na Amurka, a lokacin yakin neman 'yancin kai na Eritrea.[1]
An horar da Meki a matsayin ma’aikacin jinya a Amurka. Ya koma Eritrea ne bayan kawo ƙarshen yakin neman yancin kai da ƙasar ta yi da Habasha.[1]
An naɗa Meki kuma aka tabbatar da shi a matsayin Ministan Albarkatun Ruwa na farko bayan samun ‘yancin kai na Eritrea. Daga baya kuma ya zama Ministan Lafiya na ƙasar, kafin a sake masa muƙamin Ministan Albarkatun Ruwa a wani garambawul na majalisar ministoci. [1]
Saleh Meki ya rasu ne a ranar Juma’a, 2 ga watan Oktoba, 2009, sakamakon bugun zuciya yana da shekaru 62.[1] An binne shi a makabartar Shahidai da ke Asmara babban birnin ƙasar Eritrea. [1]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- 1 2 3 4 5 "A hero… "When you go home tell them of us and say: 'for your tomorrow we gave our today"". Shaebia. 2009-10-04. Archived from the original on 2010-10-03. Retrieved 2009-10-06.