Jump to content

Salihu Tunde Bello

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Salihu Tunde Bello
Gwamnan Jihar Kebbi

9 Disamba 1993 - 22 ga Augusta, 1996
Abubakar Musa - John Ubah
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Digiri Janar
Imani
Addini Musulunci

Kanar (Daga baya Birgediya Janar) Salihu Tunde Bello ya kasance Mai Gudanarwa a Jihar Kebbi a Najeriya daga watan Disambar shekara ta 1993 zuwa watan Agustan shekarar 1996 a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha . A lokacin mulkinsa ya samu ci gaba mai ma’ana a ɓangaren ababen more rayuwa a jihar. A watan Yulin Shekarar 1999, bayan komawar mulkin dimokuradiyya, an tilasta wa dukkan hafsoshin sojan da suka yi aikin gwamnatocin soja na tsawon watanni shida ko fiye da haka su yi ritaya. Birgediya-Janar Salihu Bello na cikin waɗanda wannan hukunci ya shafa.[1][2][3][4]

Membobin ƙungiyar kwararru

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta 2009 Salihu Bello ya kasance memba a hukumar binciken Cocoa Research Institute of Nigeria (CRIN).[5]

  1. "Nigerian States". WorldStatesmen. Retrieved 2010-01-18.
  2. Nigeria: a viable black power : resources, potentials & challenges. Polcom Press. 1996. p. 204. ISBN 978-31594-1-0.
  3. "Can a Military Coup Ever Succeed Again in Nigeria?". Max Siollun. April 11, 2008. Retrieved 2009-01-18.
  4. "OBASANJO HIRES & FIRES". NDM DEMOCRACY WATCH 1999/03. July 1, 1999. Archived from the original on December 5, 2012. Retrieved 2009-01-18.
  5. Juliana Taiwo (30 June 2009). "Yar'Adua Approves Agriculture Parastatals' Boards". ThisDay. Retrieved 2010-01-18.