Sallar Jam'i
Gabatarwa
[gyara sashe | gyara masomin]Hikimar Shar’anta sallar jam’i tana daga cikin manyan ibada da biyyana ga Allah na daga cikin abun da ya bayyana na sauki, jin kai, da kuma daidaitawa tsakanin muslmi, ta yadda suke haɗuwa a wuri karami domin sallatar salloli biyar a yini da dare, akan abin yabo tare da jagoranci guda daga cikin su, kuma a fuskanci wuri guda, sai zukata su hadu su kara haske suna masu jinka juna da saduduwa da juna kuma abin dake raba kai ya kau.[1]
Hukuncin Sallar Jam'i
[gyara sashe | gyara masomin]Sallar jam’i: Wajibi ce akan maza da suke ‘ya’ya (ba bayi ba), masu iko, mazauna a gida da kuma matafiya, domin fadin sa Allah madauka kin sarki; ﴿وَإِذَا كُنتَ فِيهِم فَأَقَمتَ لَهُمُ ٱلصَّلَوةَ ١٠٢﴾
“Kuma idan ka kasance a cikin su sai ka tsayar musu da sallah, a samu wasu bangare su tsaya tare da kai, (a wajan yaki). (Nisa’i:102).
Shi umarni yana da’idar da wajibci ne, to idan ya kasance haka za’a yi alokacin yaki to ai alokacin aminci ya fi cancanta.[2]
Wurin da ake Sallar Jam'i
[gyara sashe | gyara masomin]An sunnata ta a masalaci tare da jama’ah, kuma tana halasta a yi ta a wani wurin da ba masallaci ba idan akwai bukatar yin hakan.
Su kuma mata sun sami damar hakan idan sun kebanta ga maza, domin aikin Nana Aisha da Ummu Salama, wanda Darul-kutuni ya ambata: Kuma Manzon Allah ﷺ ya umarce Ummu Waraka da ta jagoranci mutanan gidanta. [3].