Samartaka

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Samartaka
phase of human life (en) Fassara da age of a person (en) Fassara
Bayanai
Facet of (en) Fassara development of the human body (en) Fassara
Mabiyi childhood (en) Fassara da preadolescence (en) Fassara
Ta biyo baya adulthood (en) Fassara
NCI Thesaurus ID (en) Fassara C39298
Saurayi da Budurwa
samari da yan'mata na kallon wasa

Samartaka / 'Yanmatanci suna taka muhimmiyar rawa wanda har ya kai wasu mutane na yanke hukunci da yanayin yadda mutum ya yi samartaka/yan'matancin shi/ta to haka tsufa ma zai riskeshi/ta kuma suna da muhimmanci sosai wato lokutan samartaka da ‘yan matanci.[1] Ma’anar Kalmar Samartaka Da ‘Yan matanci duk kusan daya ne muna iya cewa sa’annin juna ne samartaka wani lokaci ne da jinsin namiji yake tashen balagarsa, in mace na wannan shekarun sai a ce tana lokacin ‘yan matanci. Lokacin samartaka samari kan ji wasu dabi’u na daban misali, kamar, matsananciyar sha’awa, saboda suna kan tashen balagar fari ne don haka a wannan lokaci shi ne wanda ya fi hadari ga rayuwar samari ko kuma ‘yan mata saboda suna wasu irin dabi’u a cikin rayuwarsu kamar, jida kai, ganganci, son holewa, soyayya, kokari wajen aiki da kazar-kazar, tashen karfi, son gwaninta da burge mutane, tunba in sun ga yan'mata ba.

Mata kuwa akwai irin na su suma kamar son kwalliya, yanga, son kula maza musamman samari, jiji da kai da kuma jin isa, son girma daganin dai-dai take da kowa wato jin itama babbace da kuma tunanin saurayi ko da namiji.[2]

Hatsarin da ke cikin Lokutan Samartaka ko Yan'matanci[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai hatsarurruka manya a wannan matakin na samartaka in ba a sami kulawa ta musamman a wajen iyaye ko kuma wani mai tsawatawa ba. A wannan lokutan ne saurayi kan fara zabar abunda yake so ya zama in malami ne na addini to tun yana saurayi za ku ga ya dukufa neman ilmi kuma yana wa addini hidima in kowa dan kasuwa ne a nan ne za ku ga ya kama kasuwanci gadan-gadan. A wannan lokacin ne ake koyan shaye-shayen kwayoyi da kayan maye idan aka haɗu da miyagun abokai, a lokacin samartaka ne ake gina tsarin na rayuwa mai kyau ko marar kyau. A wannan lokacin ne ake samun dama dayawa a rayuwa sakamakon lokaci da ake da shi da kuma rashin nauyi a kai. Awannan lokaci ne kuma abubuwa na sha’awa suka mamaye zuciya kamar mata, son a yi ado na kece raini idan ana samun kudi wani lokacin ma koda ba a samu, shi kenan sai ka ga inba an dace ba rayuwa ta munana.[3]

Matsalolin da suke addabar samari[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai matsaloli masu tarin yawa da suke cutar da samari su bata musu rayuwa koma hallakasu baki daya kamar su.

 1. Rashin Sana’a Ko Hanyar Shigowar Kudi: Da zarar matashi ba shi da sana’a ko wata hanyar da kudi yake shigo masa sai ku ga ya zama abun tausayi baya iya daga hannu a cikin abokansa sannan koda yaushe yana cikin kunci, ko budurwa ma ba zai yi takirki ba sai marar aji, wasu samarin lalaci ne ke sa suki yin sana’ar, wasu kuma rashin jari, wasu kuma rashin horo da shauran su, dan haka lallai matasa a tashi a yi sana’a don a nemi halak. Domin shi kadai ne hanyar da matashi zai dogara a halin da muke cikin a yanzu.[4]
 2. Soyayya: Soyayya ita ma na daya daga cikin abunda ke kawo wa samari matsala a cikin wannan lokaci, sakamakon soyayya fal take da shashanci, shirme, takaici, bacin rai, takura, wahala, cinrai, fargaba, tunani, zancen zuci , sai kuma dan nishadi lokaci zuwa lokaci. Hakan ta sa soyayya ke shafar tunanin samari da zarar saurayi ya fara soyayya za ka ga ya tattare hankulansa ya maida shi kan masoyiyarsa idan bai yi sa’ar budurwa me kirki ba ko surukai masu kirki ba, shi kenan sai su yi ta caja masa kai. Soyayya da sha’awa tabbas nasa samari yin ta'addanci kamar kisan kai, fyade da sauran su, a karshe su jefa rayuwarsu a mugun hali wanda bai dace ba.[5]<ref name="PAmf.org">
 3. karancin Ilmi: Shi ma wannan matsalace babba da ke cutar da samari, domin ilmi shi ne hasken rayuwa kuma gishirin zaman duniya, da ilmi ne ake tinkaho a ko wane zamani domin jahilci ciwo ne, da zarar saurayi ya zama baida ilmi imma na Addini ko kuma na zamani wato boko haka zai zama me karancin amfani ga al’umma, bai san kansa ba ballantana ya san wani harma ya ba shi shawara, bai iya tsinana komai ko da kuwa wakansa, ko ga al’umma. Dan haka matasa lallai a tashi a nemi ilimin Addini da na zamani wato boko sosai ba ji ba gani, ka rage siyan sutturu ka sayi littafan addini,ko katara kudin rijista kafara karatu shi ne mafitarka a cikin wannan zamani.
 4. Iyaye: Tabbas wadansu iyaye suna daya daga cikin wadanda suke haifar da matsala ga ya’yansu samari da 'yanmata da yawan iyaye sukan kasa sauke hakkokin da Allah S W T ya dora musu na kula da ya‘yansu. Misali rashin adalci a tsakani mata guda biyu ko ya’yaye, gallazawa ya’yan kishiya, dorawa saurayi nauyin gida da zarar ya fara kawo karfi koda da uban yanada rufin asiri, din taimakawa saurayi ya yi sana’a koda yana da hankali, tilasta masa ya yi auren zumunci ko da baya bukata, rashi bashi ingartaccen ilimi. Dukka wadannan matsaloli ne na iyaye da ke shafar rayuwar samari a cikin wannan zamani. Nasiha ga iyaye lallai su ji tsoran Allah su sauke amanonin da Allah S W T ya ba su na ya’yansu, dole kabawa danka tarbiyya, koda ya balaga akwai hakkinsa a kanka na kula da shi, bashi shawarwari, nasiha, idan kana da wadata yi masa aure da wacce yake so, bashi jari idan kana da hali, sannan ka bashi ilmi. Ta haka ne zai jikan ka nan gaba.
 5. Abokai bata Gari: Suma bata garin abokai nada tasiri sosai a kan samari ko 'yanmata ta hanyar koya musu munanan dabi’u kamar sata, shaye-shaye, tunba maza ba wajen neman [[[mata]] da dai sauran su. Dan haka lallai iyaye kusa ido a kan abokan ‘ya’yanku a koda yaushe, domin abokin barawo shi ma barawo ne kuma idan kana son ka san addinin mutum ko halinsa to ka san waye abokinsa. Da yawan masu aikata munanan halaye kamar fyade, shaye-shaye, zina za ka ga batagarin abokai ne suka koya musu. Dan haka matasa ku kiyayi abokai bata-gari a hankali a hankali za su bata ka/ki idan baka an kara ba.
 6. Jagorancin 'yan siyasa da Malaman banza: Matasan Najeriya musamman ma na Arewa kashi 75 cikin dari masu son addini ne da kuma yima addini hidima da sanin ya kamata gami da son juna da hadin kai tunba matasan Fulani ba. Amma sai a samu wadansu mugayen 'yan siyasa da Malaman banza suna batar da su daga bin tafarki na daidai.
Wasu samari

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. Stehlik, Thomas (2018). Educational Philosophy for 21st Century Teachers. Springer. p. 131. ISBN 978-3319759692.
 2. Hu, Julie Xuemei; Nash, Shondrah Tarrezz (2019). Marriage and the Family: Mirror of a Diverse Global Society. Routledge. p. 302. ISBN 978-1317279846.
 3. Jaworska, Natalia; MacQueen, Glenda (September 2015). "Adolescence as a unique developmental period". Journal of Psychiatry & Neuroscience. 40 (5): 291–293. doi:10.1503/jpn.150268. PMC 4543091. PMID 26290063.
 4. "Adolescent health". www.who.int (in Turanci).
 5. Kail, RV; Cavanaugh JC (2010). Human Development: A Lifespan View (5th ed.). Cengage Learning. p. 296. ISBN 978-0-495-60037-4. Retrieved September 11, 2014.