Sarina Farhadi ( ; an haife ta 27 ga watan Afrilu shekara ta 1998) yar wasan kwaikwayo ce Yar ƙasar Iran. An haife ta ga masu shirya fina-finai Asghar Farhadi da Parisa Bakhtavar, an fi saninta da rawar da ta taka a matsayin Termeh a cikin fitaccenyan fim ɗin wasan kwaikwayo A Separation (2011), wanda ta kyautar Azurfa don Mafi kyawun Jaruma tare da ƴan wasan kwaikwayo mata.
A cikin shekara ta 2011, ta lashe Azurfa Bear don Mafi kyawun 'yar wasan kwaikwayo a Berlin International Film Festival saboda rawar da ta taka a fim ɗin mahaifinta A Separation, a matsayin Termeh . [1] Ta kuma lashe lambar yabo ta FIPRESCI don mafi kyawun 'yar wasan kwaikwayo tare da Leila Hatami da Sareh Bayat a bikin fina-finai na kasa da kasa na Palm Springs saboda rawar da ta taka a matsayin Termeh . [2]