Saud Al-Shuraim

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Saud Al-Shuraim
Saud Shuraim doing the Khutbah.png
ɗan Adam
jinsinamiji Gyara
ƙasar asaliSaudi Arebiya Gyara
sunan asaliسعود الشريم Gyara
lokacin haihuwa19 ga Janairu, 1964 Gyara
wurin haihuwaRiyadh Gyara
harsunaLarabci Gyara
sana'aLiman, judge Gyara
makarantaImam Muhammad ibn Saud Islamic University, Umm Al-Qura University Gyara
dalibiOmar al-Haddouchi Gyara
addiniSunni Islam Gyara

Saud ibn Ibrahim ibn Muhammad al-Shuraim (Larabci: سعود بن ابراهيم بن محمد الشريم،, an haife shi a 19 January 1966[1]) yana daga cikin limamai da khateeb na babban masallacin Harami (Masjid al-Haram) dake Makkah. Sananne kuma shahararren makarancin alkur'ani wato qari, yanada digirin digirgir wato digiri na uku Dakta da turanci Doctor of Philosophy|doctorate (Ph.D) kuma farfesa ne a fannin Sharia da karatun addinin Musulunci a Jami'ar Umm al-Qura a Makkah. An zabi Shuraim amatsayin Dean da kuma "Kwararren Farfesa a fikihu (Fiqh)" duk a jami'ar.[2]

Ansansa a matsayin maibincike a Fikihu. Mai shari'a ne kuma marubuci wanda yayi rubuce rubuce da dama a fannin Aqidah, filihu, da Arabic poetry. Kuma yana daga cikin manyan malaman kasar Saudiya.

Shuraim yana jagorancin sallar Taraweeh a lokutan Ramadan a Mecca, yafara tun daga 1991. Kuma yana gudanar da sallar jana'iza (Sallar mamaci) wa tsohon yarima marigayi Nayef bin Abdulaziz a 17 June 2012 bayan Maghrib (faduwar rana) a masallacin Harami.[3] Sarki Abdullah na Saudiya da yan Gidan sarautar kasar sun halarta jana'izar. Muryar sa lokacin karatu, yayadu a duniya ta fannoni daban-daban.

Anazarci[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. http://www.assabile.com/saud-shuraim-11/saud-shuraim.htm
  2. http://www.assabile.com/saud-shuraim-11/saud-shuraim.htm
  3. "Archived copy". Archived from the original on September 25, 2015. Retrieved July 1, 2016.