Sefiu Adegbenga Kaka
6 ga Yuni, 2011 - Mayu 2015 ← Ramoni Olalekan Mustapha - Buruji Kashamu → District: Ogun East | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | 14 Mayu 1952 (73 shekaru) | ||
| ƙasa | Najeriya | ||
| Harshen uwa | Yarbanci | ||
| Karatu | |||
| Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa | Action Congress of Nigeria | ||
Sefiu Adegbenga Kaka (An haifeshi ranar 14 ga watan Mayu 1952) ɗan siyasan Najeriya ne wanda ya zama Sanata mai wakiltar yankin Ogun ta Gabas daga 2011 zuwa 2015.[1] Ya taba zama mataimakin gwamnan jihar Ogun daga 1999 zuwa 2003.
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Sefiu Adegbenga Kaka a ranar 14 ga Mayun 1952, ga dangin musulmi salihai, kuma ya shiga Kwalejin Musulmi ta Ijebu a shekarar 1968.[2] Kaka ya kasance mataimakin gwamnan jihar Ogun daga 1999 zuwa 2003, a lokacin gwamnan Olusegun Osoba.[3]
Aikin Sanata
[gyara sashe | gyara masomin]A zaben da aka gudanar a ranar 9 ga watan Afrilun 2011, an zabi Kaka a matsayin Sanata mai wakiltar Ogun ta Gabas da kuri’u 76,543, inda dan takarar jam’iyyar PDP, Toheeb Odunowo ya samu kuri’u 52,613, sai dan takarar jam’iyyar Peoples Party of Nigeria (PPN), Prince Abiodun Odusanya, da kuri’u 46,148.[4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ April 9, election results and updates". Daily Triumph. 15 April 2011. Retrieved 24 April 2011.[dead link]
- ↑ Admin. "Meet Sefiu Kaka". The Scoop Ng. Retrieved 26 January 2019
- ↑ "There's No govt in Ogun, Says Osoba". Republic Report. 30 December 2010. Retrieved 24 April 2011.
- ↑ "NASS ELECTION: Heavyweights bite dust •Sheriff, Omisore, Oyinlola, Aliero, Agagu, Orji Kalu, Bankole lose". Nigerian Daily. 10 April 2011. Retrieved 24 April 2011.