Shehu Haruna Lambu
Appearance
| Rayuwa | |
|---|---|
| ƙasa | Najeriya |
| Sana'a | |
| Sana'a | ɗan siyasa |
Shehu Haruna Lambu dan siyasar Najeriya ne daga jihar Kano wanda ya zama wakilin Dawakin-Tofa/Tofa/Rimin Gado a majalisar wakilai a majalisar dokokin kasar. An zabe shi a karo na biyu a jere: daga 1990 zuwa 2003, da 2003 zuwa 2007, a matsayin dan jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).[1][2]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Shehu Haruna Lambu a watan Afrilun shekarar 1964 a jihar Kano da ke Najeriya. Ya yi Digiri na biyu a fannin Ilimi (Integrated Science) daga A.B.U. Zaria.
Fagen siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Lambu ya taba zama wakilin mazabar Dawakin-Tofa/Tofa/Rimin Gado a majalisar wakilai ta kasa na tsawon wa'adi uku a jere, daga 1990 zuwa 2003, sannan kuma daga 2003 zuwa 2007.[1][3]. Tijjani Abdulkadir Jobe ne ya gaje shi a shekarar 2007 bayan ya kammala wa’adinsa.[2]