Jump to content

Shehu Nicholas Garba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Shehu Nicholas Garba
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

11 ga Yuni, 2019 -
District: Jema’a/Sanga
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,


District: Jema’a/Sanga
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Shehu Nicholas Garba dan siyasar Najeriya ne wanda ya taba zama mamba mai wakiltar mazabar Jema'a/Sanga a majalisar wakilai. An haife shi a shekarar 1960, dan asalin jihar Kaduna ne. Ya yi karatun firamare a kwalejin Rimi Kaduna, kafin ya samu digiri na farko a fannin lissafi a jami’ar Ibadan. Ya kuma yi digirinsa na biyu a fannin banki da hada-hadar kudi daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. A shekarar 2011 aka zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai, aka sake zabe shi a 2015, sannan a 2019 kuma a karo na uku a karkashin jam’iyyar PDP.[1][2] Ya yi aiki a matsayin shugaban kwamitin yaki da cin hanci da rashawa kuma ya nada mataimaka 79 don taimakawa gwamnatinsa.[3]

  1. Citizen Science Nigeria". citizenscienigeria.org. Retrieved 2025-01-06
  2. Hon. Nicholas Shehu biography, net worth, age, family, contact & picture". www.manpower.com.ng. Retrieved 2025-01-06
  3. Nwafor (2020-06-15). "Lawmaker appoints 79 aides". Vanguard News. Retrieved 2025-01-06