Jump to content

Shugaban Alƙalan Alƙalai na Najeriya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mukala mai kyau
Shugaban Alkalan Alkalai na Najeriya
position (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na chief justice (en) Fassara
Organization directed by the office or position (en) Fassara Kotun Koli Ta Najeriya
Ƙasa Najeriya
Applies to jurisdiction (en) Fassara Najeriya

Shugaban Alkalin Alkalan Najeriya ko CJN a takaice, shine shugaban sashin shari'a na gwamnatin Najeriya, kuma shi ya ke jagorantar kotun kolin ƙasar da Majalisar Shari'a ta Ƙasa.[1] Mai shari’a na yanzu ita ce Kudirat Kekere-Ekun wacce aka naɗa a ranar 22 ga watan Agustan 2024. [2] An naɗa ta a matsayin babbar mai shari’a ta tarayyar ƙasar bayan ritayar alkalin alkalai mai ci Olukayode Ariwoola. Kotun kolin Najeriya ita ce kotun koli a Najeriya kuma duk hukuncin da ta yanke na karshe kan zama ba'a iya ja da shi, abinda ake kira kotun-da-ga kai sai Allah ya isa.[3] Shugaban alkalan Najeriya na kasancewa shugaban alƙalan biyo bayan shugaban kasar tarayyar Najeriya ya naɗa shi bisa shawarar majalisar shari'a ta kasa haka-zalika idan majalisar dattawan tarayyar Najeriya ta amince da shi ko naɗin alƙalin.[4] Kotun ta CJN tana riƙe da muƙamin ne bisa yardan tsarin mulkin Najeriya kuma ba za a iya tsige shi ba sai dai dalilin mutuwa ko kuma ya kai shekaru 70. Sai dai ana iya tsige shi ta hannun Majalisar Dattawan Tarayyar Najeriya, amman ana buƙatar samun mafi rinjayen mambobin majalisar dattawan Najeriya kafin a iya zartarwa.[5]

Sunayen shugabannin Alkalai

[gyara sashe | gyara masomin]

Ga cikakken jerin alkalan da su ka taɓa zama shugaban alƙalan alƙalai na baya-bayan nan. [6]

Shugabanin Zango/Lokaci
Sir Edwin Speed 1914–1918
Sir Ralph Combe 1918–1929
Donald Kingdon 1929–1946
Sir John Verity 1946–1954
Sir Stafford Foster-Sutton 1955–1958
Sir Adetokunbo Ademola 1958–1972
Taslim Olawale Elias 1972–1975
Darnley Arthur Alexander 1975–1979
Atanda Fatai Williams 1979–1983
George Sodeinde Sowemimo 1983–1985
Ayo Gabriel Irikefe 1985–1987
Mohammed Bello 1987–1995
Mohammed Uwais 1995–2006
Salihu Modibbo Alfa Belgore 2006–2007
Idris Legbo Kutigi 2007–2009
A. I. Katsina-Alu 2009–2011
Dahiru Musdapher 2011–2012
Aloma Mariam Mukhtar[7][8] 2012–2014
Mahmud Mohammed 2014–2016
Walter Onnoghen 2017–2019
Tanko Muhammad 2019–2022
Olukayode Ariwoola 2022–2024
Kudirat Kekere-Ekun 2024–zuwa yau

Tsofaffi Shugabannin Alkalai da Su ka Gabata

[gyara sashe | gyara masomin]
Legas (1863-1929)
  • Benjamin Way (?-1866)
  • John Carr (1866-?) (Kotun Koli na Yammacin Afirka)
  • George Faransa (1867-1874)
  • James Marshall (1874-1886)
  • Sir John Salman Smith (1886-1895)
  • Sir Thomas Crossley Rayner (1895-1902)
  • Sir William Nicholl (1902-1908)
Arewacin Najeriya
  • Alastair Davidson (1900-1901)
  • Henry Cowper Gollan (1901-1905)
  • Sir MR Menendez (1905-1908)
  • Sir Edwin Speed (1908-1913)
Kudancin Najeriya
  • Henry Green Kelly (1900-1902)
  • Willoughby Osborne (1906-1913)
  1. "Constitution". The National Judicial Council. Archived from the original on 24 January 2013. Retrieved 17 July 2012.
  2. "Senate confirms Muhammad as Chief Justice of Nigeria" (in Turanci). 17 July 2019. Retrieved 24 May 2022.
  3. "Wike: Finality of Supreme Court decision is sacrosanct". The Guardian Nigeria News – Nigeria and World News (in Turanci). 2 February 2016. Retrieved 24 May 2022.
  4. "Presidency Forwards Justice Walter Onnoghen's Name to Senate For Confirmation as CJN – PLAC Legist" (in Turanci). Retrieved 25 May 2022.
  5. "Judges retirement age and effective justice system". The Guardian Nigeria News – Nigeria and World News (in Turanci). 7 March 2021. Retrieved 24 May 2022.
  6. https://web.archive.org/web/20160220234027/http://www.fjsconline.gov.ng/list_of_chife.html Federal Judicial Service Commission, Nigeria
  7. "ALOMA MUKHTAR: Making of Nigeria's Female CJN". P.M. News. Independent Communications Network Limited. 16 July 2012. Archived from the original on 2 July 2014. Retrieved 17 July 2012.
  8. "Jonathan swears in Nigeria's first female chief justice". The Punch. Ajibola Ogunsola. 16 July 2012. Archived from the original on 17 July 2012. Retrieved 17 July 2012.

Hanyoyin haɗi na Waje

[gyara sashe | gyara masomin]