Jump to content

Sistine Stallone

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mukala mai kyau
Sistine Stallone
Rayuwa
Cikakken suna Sistine Rose Stallone
Haihuwa 27 ga Yuni, 1998 (27 shekaru)
ƙasa Tarayyar Amurka
Harshen uwa Turanci
Ƴan uwa
Mahaifi Sylvester Stallone
Mahaifiya Jennifer Flavin
Ahali Scarlet Rose Stallone (en) Fassara, Sophia Rose Stallone (en) Fassara da Sage Stallone (mul) Fassara
Karatu
Makaranta University of Southern California (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a model (en) Fassara da jarumi
Muhimman ayyuka 47 Meters Down: Uncaged (en) Fassara
The Family Stallone (en) Fassara
IMDb nm1875985

Sistine Rose Stallone (an haife ta ranar 27 ga watan Yuni, 1998) ƴar wasan kwaikwayo ce ta Amurka, mai tallar kayan ƙawa, kuma ta yi fice a ƙafafen sadarwa.[1][2] Ta fara wasan kwaikwayo a wani fim game da ban tsoro-(horror film) na shekarar 2019, mai taken 47 Meters Down: Uncaged, wanda Johannes Roberts ya bayar da umarnin shirin.[3][4] Ita ɗiyar shahararren ɗan fim kuma mai shirya fim ce, watau Sylvester Stallone wanda aka fi saninsa da sunan Rambo.

Rayuwa farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Sistine Stallone a shekara ta 1998, ita ce 'ya ta biyu ga ɗan wasan kwaikwayo- kuma darakta Sylvester Stallone da Jennifer Flavin.[5] Ita da ƴan uwanta Sophia da Scarlet sun kasance jakadunGolden Globe a lokacin bikin bayar da kyautar lambar yabo karo na 75 na Golden Globe Awards, da ya gudana a watan Janairun 2018.

A shekarar 2018, ta fara halartar Jami'ar Kudancin California domin karatun digiri a fannin sadarwa kuma ta kammala karatun.[6]

A shekara ta 2016, ta sanya hannu a IMG Models, [7] kuma ta fara fitowa a wani zane-zane na Chanel. [5] Ta bayyana a fitowar Glamour ta Yuli 2016 kuma an nuna ta a jikin bangon-(cover) Elle Russia na Nuwamban 2017. [5][8]

A 2023, Sistine Stallone ta bayyana cewar a shirin gidan talabijin na Reality Show, Mai taken The Family Stallone tana aiki a kan rubutun fim ɗin, Scavenger Hunt, fim mai ban tsoro wanda Elle Callahan ta jagoranta.[9]

Shekara Sunan fim Matsayi Bayanan kula
2019 47 Meters Down: Uncaged Nicole Fim ɗin ta na farko
2021 Midnight in the Switchgrass Heather
Shekara Sunan fim Matsayi Bayanan kula
2018 Love Advent Jaruma Episode: Sistine Stallone
2023-zuwa yau The Family Stallone Self Reality Show
  1. Wiseman, Andreas (2018-12-10). "'47 Meters Down' Sequel: Sophie Nélisse To Star, Corinne Foxx & Sistine Stallone Make Film Debuts; Summer 2019 Release". Deadline (in Turanci). Retrieved 2019-08-03.
  2. "'47 Meters Down: Uncaged' Chomps on a Final Trailer". Slanted (in Turanci). 2019-08-02. Retrieved 2019-08-03.
  3. "Sylvester Stallone's daughter Sistine Rose to debut in '47 Meters Down' sequel". The New Indian Express. 26 July 2019. Retrieved 2019-08-03.
  4. Larocca, Courteney (2019-08-01). "Sistine Stallone, 22, Sizzles In Green Gown With Thigh High Leg Slit On The Red Carpet — Pics". Hollywood Life (in Turanci). Retrieved 2019-08-03.
  5. 1 2 3 Oswald, Anjelica (5 October 2017). "Sylvester Stallone has 3 smart and stunning daughters — here's what you should know about Sophia, Sistine, and Scarlet". INSIDER. Retrieved 2019-08-12.Oswald, Anjelica (5 October 2017). "Sylvester Stallone has 3 smart and stunning daughters — here's what you should know about Sophia, Sistine, and Scarlet". INSIDER. Retrieved 2019-08-12.
  6. Antonio Stallings (2024-02-01). "Sylvester Stallone's Daughter Discovered She Lacked the Acting Gene After a Humiliating Performance". Cheatsheet (in Turanci). Retrieved 2024-11-07.
  7. "Stallone Daughters on Miss Golden Globe Gig: "This Is Our Moment"". The Hollywood Reporter (in Turanci). 5 January 2017. Retrieved 2019-08-12.
  8. Schofer, Simone (10 June 2016). "Meet Sylvester Stallone's daughter: A rising model star". Glamour UK. Retrieved 2019-08-12.
  9. Eklecty-City (2023-07-17). "Scavenger Hunt : Tout savoir sur le film de Sistine Stallone". Eklecty-City (in Faransanci). Retrieved 2023-07-17.

Hanyoyin haɗi na Waje

[gyara sashe | gyara masomin]