Sithembiso Nyoni
|
| |||||||
1 Disamba 2017 - 12 Satumba 2023
| |||||||
| Rayuwa | |||||||
| Haihuwa | 20 Satumba 1949 (76 shekaru) | ||||||
| ƙasa | Zimbabwe | ||||||
| Sana'a | |||||||
| Sana'a | ɗan siyasa da minista | ||||||
| Kyaututtuka |
gani
| ||||||
| Imani | |||||||
| Jam'iyar siyasa | ZANU-PF | ||||||
Sithembiso Gile Gladys Nyoni (an haife ta a ranar 20 ga watan Satumba 1949) 'yar siyasar Zimbabwe ce kuma a cikin shekarar 2023 ta taɓa zama ministar masana'antu da kasuwanci. Ta kasance ministar ci gaban ƙanana da matsakaitan masana'antu [1] kuma ministar harkokin mata da matasa.[2]
Aikin siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]
A zaɓen 'yan majalisa na watan Maris na 2008, an zaɓi Nyoni a matsayin 'yar majalisar wakilai a matsayin 'yar takarar jam'iyyar ZANU-PF a Nkayi ta Arewa. Ta samu kuri'u 4,634 inda ta samu kuri'u 4,234 na Moyo Talent na jam'iyyar MDC-Mutambara da 1,075 na Mlilo Thembinkosi na ɓangaren MDC-Tsvangirai.[3]
Jaridar Herald ta ruwaito a ranar 3 ga watan Janairu, 2009, cewa an kori Nyoni daga majalisar ministocin a farkon mako, tare da wasu ministoci 11, saboda ba ta da wata kujera a Majalisar.[4] A ranar 1 ga watan Disamba 2017 Shugaba Emmerson Mnangagwa ta zaɓi sabuwar majalisar ministoci, Cde Sithembiso Nyoni ta zama sabuwar ministar harkokin mata da matasa.
Ta kasance cikin jerin takunkumin Amurka tun daga shekarun 2003 har zuwa 2014.[5][6]
A cikin watan Oktoba 2023, a matsayinta na Ministar Masana'antu da Kasuwanci, tana gargadin baƙi cewa suna buƙatar lasisi don gudanar da kasuwancin dillalai. [7]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Parliament of Zimbabwe". Archived from the original on 2009-03-18. Retrieved 2008-02-06.
- ↑ "Zimbabwe: New Cabinet Appointed - Ministerial Portfolios Reduced to 22 - Only 6 Deputy Ministers Appointed". AllAfrica.
- ↑ 2008 election results Archived 2008-04-09 at the Wayback Machine, newzimbabwe.com.
- ↑ "Losing Ministers Axed", The Herald (allAfrica.com), January 3, 2009.
- ↑ Blocking property of persons undermining democratic processes or institutions in Zimbabwe
- ↑ Zimbabwe designations; Zimbabwe designations removals.
- ↑ Staff Reporter (2023-10-25). "Government targets foreigners running tuckshops in Mbare and CBD". The Zimbabwe Mail (in Turanci). Archived from the original on 2023-12-05. Retrieved 2023-12-05.