Société de Charité Maternelle
| Bayanai | |
|---|---|
| Iri | voluntary association (en) |
| Tarihi | |
| Ƙirƙira | Mayu 1788 |

Société de Charité Maternelle ko Société maternelle ƙungiya ce ta agaji ta Faransa, wadda aka kafa a shekarar 1788.
Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Anne-Françoise de Fougeret ce ta kafa ƙungiyar a Paris a watan Mayu 1788. Sai dai ba a ƙaddamar da ita a hukumance ba sai ranar 4 ga Janairu 1790, lokacin da aka gudanar da taron farko a Fadar Tuileries, a gaban Sarauniya Marie Antoinette, wadda ta amince ta zama Shugabar Girmamawa da Kafaffiyar Girmamawa, tare da zama mai kula da Société. Anne-Françoise de Fougeret ce ainihin shugaba kuma wadda ta kafa ƙungiyar. Bayan haka, ana gudanar da tarukansu akai-akai a Hôpital des Enfants Trouvés.
Manufar Société ita ce ba wa iyaye mata matalauta tallafin kuɗi, musamman iyayen jarirai. Abin da ya ƙarfafa kafa ta shi ne yadda iyaye mata matalauta suka saba kai ’ya’yansu asibitoci domin a kula da su, inda yanayin kulawar yake da muni har yawan mace-macen yara ya yi yawa. Ana ba wa mata tallafi ne bayan ƙungiyar ta bincike su ta hanyar ziyara da duba halin da suke ciki, sannan ta tabbatar cewa sun cancanci samun taimako.
Société tana daga cikin wani sabon salo na zamani na ƙungiyoyin agaji masu zaman kansu da marasa alaƙa da addini. Irin waɗannan ƙungiyoyi sun zama ruwan dare a ƙarni na 19, amma a ƙarni na 18 har yanzu sababbi ne sosai, domin a wancan lokaci Cocin ne ya fi yawan gudanar da ayyukan agaji da taimakon jama’a. Haka kuma, Société ta kasance wata sabuwar ƙirƙira saboda mata ne kaɗai ke gudanar da ita, don haka ta kasance ƙungiyar mata ta zamani wadda ba ta da alaƙa da addini, a lokacin da yawancin ƙungiyoyin mata suka kasance ƙungiyoyin addini.
An rufe Société a shekarar 1793 a lokacin Reign of Terror, amma aka sake buɗe ta a shekarar 1801. Sarki Napoleon I ya karɓi iko da Société a shekarar 1810, ya mayar da ita wata babbar ƙungiya da ke haɗa sauran ƙungiyoyi, inda ya shigar da duk sauran irin ƙungiyoyin agajin mata na Faransa a cikinta, sannan ya naɗa Empress Marie Louise a matsayin Shugabar Girmamawa.
Société ta ci gaba da samun kariya daga gwamnati tare da kasancewa ƙarƙashin kulawar mata daga gidan sarauta a gwamnatocin Faransa da suka biyo baya: Marie-Thérèse, Duchess of Angoulême ce ta kula da ita har zuwa 1830; Maria Amalia of Naples and Sicily ta kula da ita a lokacin July Monarchy; sannan Eugénie de Montijo ta kula da ita a lokacin Second French Empire..