Struggle Front for the National Independence of Guinea
| Bayanai | |
|---|---|
| Gajeren suna | FLING |
| Iri | jam'iyyar siyasa |
| Ƙasa | Guinea-Bissau |
| Tarihi | |
| Ƙirƙira | 3 ga Augusta, 1962 |
| Founded in | Dakar |
Ƙungiyar Gwagwarmayar neman 'Yancin Ƙasa ta Guinea (Portuguese: Frente de Luta pela Independência Nacional da Guiné, Portuguese Frente Luta pela Independência Nacional da Guiné, FLING) wani yunkuri ne na siyasa a Guinea-Bissau. Ƙungiyoyi masu adawa da koyarwar Marxist na Amílcar Cabral da Jam'iyyar Afirka don neman 'Yancin Guinea da Cape Verde (PAIGC) ne suka kafa, FLING ya taka muhimmiyar rawa a gwagwarmayar 'yanci na ƙasa da 'yan mulkin mallaka na Portugal.[1][2]
Kungiyar kwadago ta ƙasa União Geral dos Trabalhadores de Guiné Bissau tana da alaƙa da FLING a lokacin kafin samun yancin kai.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]An kafa FLING a Dakar, Senegal a ranar 3 ga watan Agusta 1962 a matsayin ƙawancen jam'iyyu bakwai, ciki har da Ƙungiyar 'Yanci ta Guinea, Ƙungiyar Jama'ar Guinea da Ƙungiyar 'Yan Asalin Guinee na Portuguese. Ba kamar jam'iyyar PAIGC ba, ta yi kira da a raba Guinea-Bissau da tsibiran Cape Verde, kuma ta sami goyon baya daga 'yan ƙasashen waje na Manjack a Senegal, Faransa da Gambia.[1]
Ta gudanar da wasu ayyukan soji a kusa da kan iyakar arewa kusa da Susana da São Domingos a farkon shekarun 1960, amma bayan da suka yi tir da yunƙurin haɗaka da kungiyar ta PAIGC, ƙungiyar ba ta taka rawar gani ba a yakin 'yancin kai. PAIGC ta ga FLING a matsayin barazana kuma an tsananta wa membobinta da ƙarfi, kuma a wasu lokuta, an kashe su.[1][2]
Lokacin da aka gabatar da siyasar jam'iyyu da yawa a cikin shekarar 1990s, FLING ta halatta a ranar 24 ga watan Mayu 1992. Ta yi takara a babban zaɓe na shekarar 1994 kuma ta sami kujera a Majalisar Jama'ar Ƙasa. A zaɓukan shugaban ƙasa ta sanya a gaba François Mendy, wanda ya kasance shugabanta tun a shekarun 1960. Mendy ya zo na biyar da kashi 3 cikin 100 na kuri'un da aka kaɗa, amma ya samu kujerar majalisar wakilai ta jam'iyyar.[1][2]
Rikicin shugabanci ya ga José Catengul Mendes ya zama jagora ta zaɓen 1999. Jam'iyyar ta rasa kujerar ta a Majalisar, kuma Mendes ya zo na goma a zaɓen shugaban ƙasa da kashi 1.4% na kuri'un da aka kaɗa. A shekara ta 2003 jam'iyyar ta shiga kawancen United Platform, wacce ta yi takara a zaɓen Majalisar 2004, amma ta ƙasa samun kujera.[1][2]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Benjamin Pinto Bull