Jump to content

Sulaiman Abdul Aziz Al Rajhi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sulaiman Abdul Aziz Al Rajhi
Rayuwa
Haihuwa Saudi Arebiya, 30 Nuwamba, 1928
ƙasa Saudi Arebiya
Mazauni Jeddah
Ƙabila Saudis (en) Fassara
Harshen uwa Larabci
Mutuwa 2017
Ƴan uwa
Yara
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a Entrepreneur, Ma'aikacin banki da ɗan kasuwa
Kyaututtuka
Imani
Addini Mabiya Sunnah

Sheikh Sulaiman bin Abdulaziz Al Rajhi ( Larabci :سليمان بن عبد العزيز الراجحي, an haife shi a shekara ta 1929)[1] ɗan kasuwa ne da ke a ƙasar Saudiyya. A shekarar 2011, Forbes ta kiyasta dukiyarsa da ta kai dala biliyan 7.7, wanda hakan ya sa ya zama mutum na 120 mafi arziki a duniya.[2]

Ya samu lambar yabo ta Sarki Faisal ta ƙasa da ƙasa a shekarar 2012 saboda sadaukar da rabin dukiyarsa ga ayyukan agaji, buɗe bankin Musulunci, tallafawa ayyukan agaji da aiwatar da ayyukan ƙasa masu inganci.[3]

Tarihin Rayuwarsa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Sulaiman Al Rajhi a garin Al Bukairiyah da ke lardin Al Qassim a ƙasar Saudiyya, kuma ya taso ne a cikin sahara na Nejd inda shi da ɗan'uwansa Saleh suka fara sana'arsu ta hanyar karɓar kuɗi ga mahajjata masu safarar raƙumi da suke ƙetarawa cikin sahara zuwa garuruwan Makka da Madina.

Sulaiman Abdulaziz Al Rajhi ne ke da hannun jari mafi girma a bankin Al Rajhi na iyalinsa, wanda a ko da yaushe ya ba da rahoton ayyukan da suka fi samun riba a tsakanin dukkanin ƙungiyoyin bankunan Saudiyya. Wanda ya kafa bankin, tare da babban yayansa, Saleh, a halin yanzu shi ne shugaban abin da aka amince da shi a matsayin babbar cibiyar Tadawul.

Haɓakar kasuwancin 'yan'uwan Al Rajhi da faɗaɗa ya samu ne sakamakon kwararar ma'aikata masu yin ƙaura zuwa Saudi Arabiya a lokacin da aka haƙo mai na 1970s. Al Rajhis ya taimaka musu aika abin da suke samu gida zuwa wurare kamar Indiya da Pakistan. A shekarar 1

Iyalan Al Rajhi sun ci gaba da kasancewa masu hannun jari na Bankin Al Rajhi duk da cewa Sulaiman da 'yan uwansa sun raba jarin iyali zuwa gypsum, noma, ƙarfe, da sauran sassan masana'antu.

Karatun digiri na farko na karatunsa shine digirin Elamentari na farko. Yana zaune a Saudiyya kuma yana da yara aƙalla 23. [4]

Aikin Taimakonsa

[gyara sashe | gyara masomin]

Iyalan Al Rajhi, galibi a Saudi Arabiya ana ɗaukar su a matsayin mafi arziki a ƙasar waɗanda ba ƴan gidan sarauta ba, kuma cikin manyan masu bayar da agaji a duniya.

Ya kafa Jami'ar Sulaiman Al Rajhi a garinsu, jami'ar da ba ba'a karɓar kuɗi. Babban abin da jami'ar ta fi mayar da hankali a kai shi ne kiwon lafiya da harkokin banki na Musulunci, amma kuma tana ƙunshe da wasu darussa.

A cikin watan Mayun 2011, ya sanar da cewa yana ba da gudummawar mafi yawan dukiyarsa dala biliyan 7.7 ga sadaka.

  1. "اﻟﻤﺆﺳﺲ ﺳﻠﻴﻤﺎﻥ اﻟﺮاﺟﺤﻲ – شركة أوقاف سليمان الراجحي القابضة". www.asrhc.com (in Larabci). 19 December 2016. Retrieved 30 June 2017.[permanent dead link]
  2. "Sulaiman-al-rajhi's life rags riches story".[permanent dead link]
  3. "King Faisal International Prize". Archived from the original on 2013-08-11.
  4. "Sulaiman Bin Abdul Al Rajhi". Forbes. 2004. Retrieved 2011-05-16.