Sunayen Ranaku

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Sunan rana)
laƙabi
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na suna da name particle (en) Fassara

Ranakun mako da sunan mutanen da ake yi ma laƙabi dasu

Rana Mace Namiji
Lahadi Ladi,Ladidi Ɗanladi
Litinin Altine,tinene Ɗanliti
Talata Talatu,Talatuwa Ɗantala
Laraba Balaraba Balarabe
Alhamis Lami Ɗanlami
Juma'a Jummai,Jumala Ɗanjummai
Asabar Asabe Ɗan asabe

Sunan Rana Kamar yadda ƙabilu da al'adu ke da sunaye daban-daban da dalilin sanya su, sunan rana na ɗaya daga cikin sunayen da Hausawa ke yin laƙabi da su. Sunan rana shi ne sunan da ake ba mutum laƙabi dashi akan ranar da aka haifi mutum a ita, mace ko namiji kamar yadda muke da kwanakin mako guda Bakwai:

  1. Lahadi
  2. Litinin
  3. Talata
  4. Laraba
  5. Alhamis
  6. Juma'a
  7. Asabar
Wadannan sune sunayen kwanakin mako a Hausa.

Sunayen dake sama sune sunayen ranakun da akeyin laƙabi da su