Susan Grey Akers
|
| |
| Rayuwa | |
| Haihuwa |
Richmond (en) |
| ƙasa | Tarayyar Amurka |
| Mutuwa |
Chapel Hill (en) |
| Karatu | |
| Makaranta |
University of Wisconsin–Madison (en) UChicago (mul) University of Kentucky (en) |
| Harsuna | Turanci |
| Sana'a | |
| Sana'a |
librarian (en) |
| Employers |
University of North Carolina at Chapel Hill (en) |
| Kyaututtuka |
gani
|
Susan Grey Akers (April 3, 1889 – January 30, 1984) ta kasance ma'aikaciyar laburare 'yar Amurka kuma mace ta farko da ta rike mukamin deen a Jami'ar North Carolina.
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Akers a Richmond, Kentucky, ga iyaye Clara Elizabeth Harris da James Tazewell Akers, farfesa harshe ce a Jami'ar Kentucky.[1] Ta sami digiri na farko a harshen Latin da Girkanci daga Jami'ar Kentucky a 1909,[1] bayan haka ta koyar da Latin na shekara ɗaya a makarantar sakandare a Kentucky, sanan 'yan aji biyar da shida a Birmingham, Alabama na tsawon shekara daya.[2] A cikin 1911, ta fara aiki a laburare na jama'a a Louisville, Kentucky, ta ci gaba da zuwa Makarantar Laburare a Jami'ar Wisconsin a 1913,[3] inda ta yi abota da darekta Mary Imogene Hazeltine.[1]
Bayan ta sami takardar shedar zama ma’aikaciyar laburare kuma mataimakiyar mai kula da kwalejin Wellesley a Sashen Tsabta da Ilimin Jiki inda ta sake tsarawa da sabunta tsarin tattara kasidu. A lokacin bazara, ta yi aiki a Laburaren Jama'a na New York tana aikin shirya kasidu.[1] A cikin shekarar 1927, ta rubuta Salon Shirya ƙasidu cikin Sauƙi wanda aka buga har sau bakwai, tare da kowane sabon bugu yana nuna sabbin hanyoyin koyarwa, na tsawon rayuwarta.[1][4]
Ta shiga Makarantar Laburare ta 'Yan Jami'a a Jami'ar Chicago a 1927 inda ta yi karatu a karkashin Harriet E. Howe da Douglas Waples. Binciken ta ya nuna sha'awarta ga shirya kasida da kuma damuwarta cewa yawancin masu kula da dakunan karatu suna tunanin cewa ba ta da kyau, ta zama ta farko wadda ta ba da shawarar yin cikakken bayani game da littattafai da ba dole ba, sai dai inda ya dace. Ta kammala karatun digirinta na uku a shekarar 1932
Takardu
[gyara sashe | gyara masomin]Takardun Susan Gray Akers, 1899-1984, tarin ana ajiye su a cikin ɗakin karatu na Musamman na Louis Round Wilson a Jami'ar North Carolina. Kimanin abubuwansa 1,200 wani yanki ne na Tarin Tarihi na Kudancin[5].
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 1]Davis, Donald G. (2003). Dictionary of American Library Biography: Second supplement. Libraries Unlimited. ISBN 9781563088681.
- ↑ Kelling, Lucile (August 29, 1954). "Dean Akers Retiring From University Faculty". Rocky Mount Telegram. North Carolina, Rocky Mount. p. 3. Retrieved 20 April 2019 – via Newspapers.com.
- ↑ "Susan Grey Akers Papers, 1899-1984". finding-aids.lib.unc.edu. Retrieved 2019-01-07.
- ↑ Charles, Dorothy (January 1945). "Reviews: Simple Library Cataloging. Susan Grey Akers". doi:10.1086/617079. Cite journal requires
|journal=(help) - ↑ [3]"Susan Grey Akers Papers, 1899-1984".