Susan Lakot
| |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa |
Kitgum District (en) | ||
| Karatu | |||
| Makaranta | Jami'ar Kyambogo | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | soja | ||
Lt Col Susan Oruni Lakot, malama ce 'yar ƙasar Uganda kuma jami'iyar soja, wacce ke aiki a matsayin zaɓaɓɓiyar 'yar majalisa mai wakiltar Sojojin Uganda (UPDF) a majalisar ta 10 (2016-2021). [1]
Tarihi da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haife ta a ranar 7 ga watan Yuli, 1975, a gundumar Kitgum, a cikin yankin Arewacin Uganda. Ta halarci makarantar firamare ta jama'a ta Kitgum, don karatun firamarenta. Daga nan ta tafi "YY Okot Memorial College" da ke Kitgum, inda ta kammala karatunta na O-Level. Ta samu Diploma, bayan ta kammala karatunta na A-Level a Makarantar Sakandare ta Bukoyo, a Garin Iganga, a shekarar 1993. [1]
An shigar da ita Kwalejin Malamai ta ƙasa (yanzu ɓangaren Jami'ar Kyambogo), ta kammala a shekarar 1999, tare a fannin Diploma a Sakandare. Shekaru goma bayan haka, ta kammala karatun digiri na farko a Jami'ar Ndejje. [1]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Dangane da tarihin rayuwarta a shafin yanar gizon majalisar dokokin Uganda, Susan Lakot ta fara koyarwa a makarantar sakandaren sojoji ta Bombo, a shekarar 2003, a matsayin malamar farar hula.[2] [3] Bayan shekaru uku, sai aka kara mata girma zuwa muƙamin mataimakiyar shugabar malamai a makarantar, har yanzu tana farar hula. [1]
Ta shiga UPDF a shekarar 2010. A wannan shekarar, an tura ta zuwa Kwalejin Ƙananan Ma’aikata ta Uganda, a Jinja, gundumar Jinja, a yankin Gabashin Uganda. A cikin shekarar 2011, an zaɓe ta zuwa majalisa ta 9 (2011-2016). A cikin shekarar 2016, an sake zaɓen ta zuwa majalisa ta 10 (2016-2021). [1] [2] [3]
Iyali
[gyara sashe | gyara masomin]Manjo Susan Lakot na auren Sajan Robert Abok, wani jami'in rundunar 'yan sandan Uganda. [1] [4]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Sojojin Uganda
- Flavia Byekwaso
- Jerin sunayen 'yan majalisar dokoki na goma na Uganda
- Majalisar Uganda
- Rundunar Sojojin Uganda
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 1.5 Parliament of Uganda (2019). "Parliament of Uganda Members of the 10th Parliament: Lakot Susan Oruni". Parliament of Uganda. Retrieved 11 February 2019.
- ↑ 2.0 2.1 Kasasira, Risdel (6 March 2016). "Who are new UPDF MPs?". Retrieved 11 February 2019.
- ↑ 3.0 3.1 Richard Wanambwa (3 March 2016). "UPDF elects MPs today". Eagle Uganda. Retrieved 11 February 2019.
- ↑ Edge Reporter (16 December 2018). "Police Sergeant weds UPDF Major". The Edge Uganda. Archived from the original on 12 February 2019. Retrieved 11 February 2019.