Jump to content

Swinthin Maxwell Arko

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Swinthin Maxwell Arko
Member of the 2nd Parliament of the 1st Republic of Ghana (en) Fassara

9 ga Yuni, 1965 - 24 ga Faburairu, 1966
Election: 1965 Ghanaian parliamentary election (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Nsaba (en) Fassara, 21 ga Maris, 1920
Mutuwa 2006
Karatu
Makaranta Mfantsipim School (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Kiristanci
Jam'iyar siyasa Convention People's Party (en) Fassara

Swithin Maxwell Arko (1920-2006) ɗan siyasar ƙasar Ghana ne a jamhuriya ta farko. Ya kasance ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Agona nsaba daga shekarun 1965 zuwa 1966. [1] Kafin shiga majalisar ya kasance shugaban ƙaramar hukumar Agona sannan kuma shugaban kungiyar ƙananan hukumomi ta ƙasa.

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Arko a ranar 21 ga watan Maris 1920 a Nsaba, wani gari a yankin Tsakiyar Ghana. [2] Ya yi karatu a Nsaba Presbyterian Middle Boarding School da Mfantsipim School, Cape Coast. Ya zarce ƙasar Ingila inda ya karanci ƙananan hukumomi bayan ya yi aiki da UAG Ltd na kimanin shekaru goma. [3]

Aiki da siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Arko ya fara aiki tare da U. A. G. Ltd daga shekarun 1941 har zuwa 1951 lokacin da ya tafi Ingila don ƙarin karatu.[3] Bayan ya dawo Ghana a shekarar 1952, ya yi aiki a Majalisar Ƙaramar Hukumar Agona a matsayin magatakarda na majalisar. A shekara ta 1957 ya shiga Hukumar Kasuwancin Cocoa a matsayin babban jami'in rance. Ya yi aiki tare da Kwamitin Kasuwancin Cocoa har zuwa shekara ta 1962 lokacin da ya zama shugaban Majalisar Ƙaramar Hukumar Agona da mataimakin shugaban Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi.[4][5] Daga baya ya zama shugaban kungiyar National Association of the Local Government Council. [6] Ya kuma kasance memba na zartarwa na Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi ta Afirka kuma memba na zattara na Ƙungiyar Hukumomin Ƙananan Hukumomin Duniya.[7][8] A watan Yunin 1965 ya zama memba na majalisa na mazaɓar Agona Nsaba.[9][10] Ya yi aiki a wannan matsayin har zuwa watan Fabrairu 1966 lokacin da aka hambarar da Gwamnatin Nkrumah.

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Arko ya rasu a shekarar 2006 kuma ya bar ‘ya’ya bakwai. Abubuwan sha'awarsa sun haɗa da karatu da ƙwallon ƙafa. [11]

  • Jerin sunayen 'yan majalisar da aka zaba a zaben 'yan majalisar dokokin Ghana na 1965
  1. "Parliamentary Debates; Official Report, Part 2". Parliamentary Debates. Ghana National Assembly: iii and 8. 1965.
  2. "Ghana Year Book". Ghana Year Book. Graphic Corporation: 4. 1966.
  3. 3.0 3.1 "Ghana Year Book". Ghana Year Book. Graphic Corporation: 204. 1966. Cite error: Invalid <ref> tag; name "ARKO" defined multiple times with different content
  4. "Executive Instruments". Executive Instruments. Ghana Publishing Company: 82. 1962.
  5. "Ghana Today, Volume 7". Ghana Today. Information Section, Ghana Office: 13. 1963.
  6. "Local Government Throughout the World, Volume 5". Local Government Throughout the World. James Clarke: 2. 1966.
  7. "Ghana Year Book". Ghana Year Book. Graphic Corporation: 204. 1966.
  8. "Ghana Year Book". Ghana Year Book. Graphic Corporation: 204. 1966.
  9. "Ghana Year Book 1966". Ghana Year Book. Daily Graphic: 22. 1966.
  10. "West Africa Annual, Issue 8". West Africa Annual. James Clarke: 79. 1965.
  11. "Ghana Year Book". Ghana Year Book. Graphic Corporation: 204. 1966.