Tabrett Bethell
|
|
|
| Rayuwa | |
|---|---|
| Haihuwa | Sydney, 13 Mayu 1981 (44 shekaru) |
| ƙasa | Asturaliya |
| Harshen uwa |
Australian English (en) |
| Karatu | |
| Harsuna | Turanci |
| Sana'a | |
| Sana'a |
jarumi, model (en) |
| Tsayi | 173 cm |
| IMDb | nm3248988 |
Tabrett Bethell (an haife ta ranar 13 ga watan Mayu, 1981)[1][2] tsohuwar ƴar wasan kwaikwayo ce ta Australiya, wacce aka fi sani dalilin irin rawar da ta taka a matsayin; Cara Mason, a cikin jerin shirye-shiryen talabijin mai suna; Legend of the Seeker. Kafin aikin fara fitowa a fina-finai, ta yi aiki a matsayin mai tallata kayan ado tun tana ƴar shekara 16,[1] kuma shugaba ce, ga ƙungiyar Rugby League ta Cronulla-Sutherland Sharks har ya zuwa shekarar 2006.[3]
Ayyukan wasan kwaikwayo
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan farkon shekarun da ta fara tallar kaya, da kuma shugabancin da ta yi, ta yanke shawarar ci-gaba da koyan aikin fim a Screenwise, inda ta kammala biyo bayan shafe watanni 12 a shekara ta 2007. [4] A lokacin wannan horo ta ci gaba da tallata kayan kawa. [5] Shirin wasan kwaikwayonta na farko sun haɗa da fitowa a matsayin; Amy a fim ɗin Campbell Graham, mai taken Anyone You Want-(Duk wanda kuke So), da kuma rawarta a matsayin Chris a fim ɗin Strangers Lovers Killers, wanda aka fitar a shekarar 2010.
Daga 2009 ya zuwa 2010, Bethell ta yi fim ɗin talabijin mai dogon zango; Legend of the Seeker, wani shirin talabijin wanda kacokan ya ta'allaka ne akan labarin Terry Goodkind's Sword of Truth. Ta fito a mai suna Cara Mason wanda ta bayyana a ƙarshen zangon wasa na farko a shirin kafin ta bayyana sosai a fitowar zango na zama na 2 na shirin mai dogon zangon.[6] Bethell ta sami ɗumbin magoya bayan dalilin irin rawar da ta taka a matsayin Cara Mason a shirin mai taken; Legend of the Seeker.
Bayan fim ɗin Legend of the Seeker, Bethell ta fito a matsayin Beth a fim ɗin James Rabbitts' Australian thriller, mai taken; The Clinic, wanda aka ɗauki shirya fim ɗin a Deniliquin, NSW, Austaraliya a watan Nuwamban 2008. A watan Agustan shekarar 2010 Bethell ta lashe kyautar ƴar wasan kwaikwayo mafi kyau a bikin fina-finai na Manhattan saboda rawar da ta taka a fim ɗin Anyone You Want.[7]
A watan Maris na shekara ta 2011, ta fito a shirin kamfanin Warner Bros TV pilot, "Poe" a matsayin wacce ta taka rawar Sarah Elmira Royster.[8][9]
Tabrett Bethell ta fara fitowa a fina-finan masana'antarBollywood ta ƙasar Indiya, a wani fim din Hindi; Dhoom 3 wanda aka saki a ranar 20 ga watan Disamba, 2013. Inda ta haɗe da taurarin Indiya, irin su; Aamir Khan da Katrina Kaif a kashi na 3 na fim ɗin, biyo bayan fim ɗin Dhoom, wanda ba ta fito a cikin kashi na 1 da na 2 ba.[10] Fim din ya zama Fim ɗaya tilo na Bollywood mafi girma a samun riba a kasuwar duniya gaba-daya daga wannan masana'anta. [11] [12][13][14]Ta ɗan fito kaɗan a zango na 2, kashi na 6, na fim ɗin ("What Do You Really Want"), a matsayin Kate . An haska fim ɗin a ranar 7 ga watan Yulin shekarar 2014. A watan Maris na shekara ta 2014 an sanya ta a wani gajeren fim mai zaman kansa; Oren a matsayin wacce ta jagoranci fim ɗin a shirin fim din-(lead actress). Fim din ya lashe kyaututtuka biyu a bikin Hollywood Reel Independent Festival na 2015 Mafi kyawun Actress Tabrett Bethell da Mafi kyawun gajeren Fim na Duniya.
Fitowar karshe da tayi a fim, shi ne a kakar 2016 na shirin; Mistresses. [15]
Rayuwa ta Musamman
[gyara sashe | gyara masomin]An sanya mata sunan Bethell ne, inda sunan ya samo asali daga wani titi a Sydney; Tabrett Street, wani abu da ya haifar da hakan, shi ne a lokacin da iyayenta ke gardamar wane suna za su sanya mata a lokacin suna a asibiti (mahaifiyarta na son a sanya mata "Siobhan", a hannu guda mahaifinta na so a kira ta da; "Murray"). Mahaifinta ya fita motsa jiki, inda ya yi arba da sunan wannan titi, kumawarsa ke da wuya a asibitin, ya yanke shawara ga mahaifiyarta, wacce ta ce, "hakan yayi mata ita ma!".[16]
Jadawalin Fim
[gyara sashe | gyara masomin]| Shekara | Suna | Matsayi | Bayanan kula |
|---|---|---|---|
| 2001 | Life Support[17] | Episode #1.2 (3 Sep 2001) | |
| 2007 | Mr. Right[18] | Lead | Video short |
| 2007 | The Swallow[19] | Veronika Le'Morel, the beggar | Short Film |
| 2007 | Strangers Lovers Killers[20] | Chris | Film |
| 2009–2010 | Legend of the Seeker | Cara Mason | 23 episodes |
| 2010 | The Clinic | Beth Church | Film |
| 2010 | Anyone You Want | Amy | Film |
| 2010 | Cops LAC | Eve Louizos | Episode: "Life is a Rodio" |
| 2011 | Poe[21] | Sarah Elmira Royster | Pilot |
| 2012 | Sanctuary[22] | Lia | Short Film |
| 2013 | Dhoom 3[23] | Victoria | Indian film |
| 2014 | Oren | Emile | Short Film |
| 2014–2016 | Mistresses | Kate Davis | Episode 02x06: "What Do You Really Want" Series regular (Series 4 Episode 2–13) |
Gidan wasan kwaikwayo
[gyara sashe | gyara masomin]| Shekara | Suna | Matsayi | Bayanan kula |
|---|---|---|---|
| 2008 | Somewhere between the Sky and the Sea[24] by Alex Broun | Stephanie | Short and Sweet Sydney |
| 2012 | Savage in Limbo[25] |
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "Head Spinner". Ralph. October 2002. p. 106. Archived from the original on 16 May 2014.
This 21-year-old … with five years modeling experience.
- ↑ "Tabrett Bethell: "This is 40!"". Instagram. Archived from the original on 24 August 2022. Retrieved 13 May 2021.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
- ↑ "Tabrett Bethell Cheerleader". tabrettbethell.info. 28 May 2009. Archived from the original on 10 October 2009. Retrieved 28 May 2009.
Tabrett Bethell (Sharks) used to be a cheerleader for the NRL (National Rugby League) Cronulla Sharks.
CS1 maint: unfit url (link) - ↑ "A Star set to Shine". Industry Heartbeat. Screenwise. 5 December 2007.
- ↑ "Image Details". NewsPhotos.com.au. 21 February 2007.[permanent dead link]
- ↑ "Characters". Legend of the Seeker homepage. 2009.
- ↑ "Best Actress". CaptivatedByTabrett.com. Aug 2010. Archived from the original on 22 September 2010.CS1 maint: unfit url (link)
- ↑ "Tabrett cast in pilot TV show: 'Poe'". CaptivatedByTabrett.com. Mar 2011. Archived from the original on 30 June 2012.CS1 maint: unfit url (link)
- ↑ "'Poe' is dead". CaptivatedByTabrett.com. May 2011. Archived from the original on 14 August 2011.CS1 maint: unfit url (link)
- ↑ "Tabrett Bethell to Join Aamir Khan and Katrina Kaif in Dhoom 3: Back in Action". invectura.com. 28 September 2012. Archived from the original on 14 April 2018. Retrieved 21 January 2013.
- ↑ "Top Ten Overseas Grossers 2014 – Jai Ho Tops The Charts". Box Office India. Archived from the original on 23 September 2015. Retrieved 29 May 2014.
- ↑ "Dhoom 3: 7th Weekend Overseas Box Office Collections". Koimoi.com. 4 February 2014. Retrieved 30 April 2014.
- ↑ "South Indian films dominate international markets!". Bollywood Hungama. Archived from the original on 15 January 2014. Retrieved 14 January 2014.
- ↑ "Dhoom 3 Is Highest Ever Grosser Overseas". Box Office India. Archived from the original on 13 January 2014. Retrieved 8 January 2014.
- ↑ "Mistresses Season 4: Alyssa Milano Still Out, [Spoiler] Back as Series Regular!". 19 February 2016.
- ↑ Hartinger, Brent (24 February 2010). "Tabrett Bethell is Not Cara (or IS She?)". TheTorchOnline.com. Archived from the original on 26 February 2010.
Well, my birthday is in May, which means I’m a Taurus.
- ↑ "Life Support Episode #1.2 (TV episode 2001) – IMDb". IMDb.com.
- ↑ "Tabrett Bethell Stars In Mr Right". TabrettBethell.info. 2009. Archived from the original on 27 November 2009.CS1 maint: unfit url (link)
- ↑ "The Swallow – IMDb". IMDb.com.
- ↑ "Tabrett Bethell Bio". CaptivatedByTabrett.com. Archived from the original on 2 January 2013.CS1 maint: unfit url (link)
- ↑ "Tabrett Bethell Cast in Poe". CaptivatedByTabrett.com. Archived from the original on 30 June 2012.CS1 maint: unfit url (link)
- ↑ "Tabrett Bethell in Sanctuary". CaptivatedByTabrett.com. Archived from the original on 10 July 2012.CS1 maint: unfit url (link)
- ↑ "Australian actress joins Dhoom 3 cast". timesofap.com. 28 September 2012.
- ↑ "2008 Top 90 Seymour Centre Week 5". Short+Sweet Sydney 2008. February 2008. Archived from the original on 21 March 2012.
- ↑ "Tabrett in Savage in Limbo8". Archived from the original on 16 June 2013.CS1 maint: unfit url (link)
Adireshin Waje
[gyara sashe | gyara masomin]- Tabrett Bethell on IMDb

- "Tabrett Bethell". Chadwick Models. 2007–2011. Archived from the original on 26 July 2011. Retrieved 24 June 2009.
- Tabrett Bethell on Twitter

- Tabrett Bethell on Instagram

- CS1 maint: BOT: original-url status unknown
- CS1 maint: unfit url
- All articles with dead external links
- Articles with dead external links from September 2025
- Articles with invalid date parameter in template
- Articles with permanently dead external links
- Muƙaloli masu kyau
- Articles with hCards
- Wikipedia articles with ISNI identifiers
- Wikipedia articles with LCCN identifiers
- Wikipedia articles with VIAF identifiers
- Wikipedia articles with WorldCat-VIAF identifiers
- Rayayyun mutane
- Haifaffun 1981