Tafkin Maladumba
Appearance
| Tafkin Maladumba | |
|---|---|
|
| |
| General information | |
| Height above mean sea level (en) | 408 m |
| Tsawo | 5 km |
| Labarin ƙasa | |
![]() | |
| Tsarin Daidaiton Labarin Kasa | 11°13′48″N 10°21′54″E / 11.23°N 10.365°E |
| Kasa | Najeriya |
Tafkin Maladumba tafki ne da ke cikin jihar Bauchi Na Najeriya.
Wuri
[gyara sashe | gyara masomin]Tafkin na a yankin arewacin Jos Plateau, kimanin nisan kilomita 120 daga arewa maso gabashin birnin Bauchi, kilomita 18 kudu maso yammacin Misau, da kuma kilomita 2 a yammacin Shelon, wani karamin ƙauyen kamun kifi. Tafkin ne mai zurfi, tare da matsakaicin zurfin kimanin mita biyu, kuma yana kwance a gefen kogin Kuka, wanda ke fita daga tafkin a matsayin Kogin Kari. Wannan wani yanki ne na Komadugu Gana, kuma saboda haka tafkin yana cikin tsarin kogin Komadugu Yobe, wani kogi a cikin Tafkin Chadi wanda har zzuwa shekarun 1980 ya gudana cikin Tafkin Chadi.[ana buƙatar hujja]
