Jump to content

Tania Leon

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Tania Leon
Rayuwa
Cikakken suna Ruth Naomi Leon
Haihuwa Wellington (en) Fassara, 4 Mayu 1945
ƙasa Afirka ta kudu
Mutuwa Utrecht (mul) Fassara, 15 ga Augusta, 1996
Karatu
Makaranta Athlone Institute of Technology (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a gwagwarmaya, Mai kare hakkin mata da anti-apartheid activist (en) Fassara

Tania Leon, haifaffen Ruth Naomi Leon, ( Wellington, 4 ga Mayu, 1945 – Nigtevecht, Agusta 15, 1996) haifaffiyar Afirka ta Kudu malama ce kuma yar gwagwarmayar kare mata. Ta kasance memba na ƙungiyar yaƙi da nuna wariyar launin fata a Netherlands da kuma ƙungiyar ANC ta Holland. [1]

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Leon ranar Juma'a 4 ga watan Mayu, 1945 a Wellington, Afirka ta Kudu. Ita ce auta a cikin iyali guda tara. [1] Leon ta sami horo a matsayin malama kuma a cikin shekara ta ilimi 1960-1961 ta sami "takardar shedar malamar firamare" a Cibiyar Athlone a Paarl, Afirka ta Kudu. Daga watan Janairu 1969 zuwa watan Yuni 1972 ta yi aiki a matsayin mataimakiyar koyarwa a Makarantar Sakandare ta Mountain River a Wellington. [1]

A shekara ta 1973, Leon ta yanke shawarar barin Afirka ta Kudu saboda manufofin gwamnatin Afirka ta Kudu na nuna wariyar launin fata na kara zama danniya. Ta isa Netherlands a shekarar 1973. [1]

Leon ta ci gaba da karatun aikin jinya a Amsterdam daga shekarun 1973 zuwa 1976 kuma ta yi aiki daga watan Agusta 1982 har zuwa farkon shekara ta 1985 a matsayin ma'aikaciyar jinya ta gundumar Amsterdam Cross Societies. Ta zama 'yar ƙasar Holland a shekarar 1984. [1]

Leon ta yi aiki daga watan Agusta 1986 zuwa 1989 a Foundation for Women and Informatics a Amsterdam, haka kuma malama a Makarantar Informatics na Mata daga Agusta 1987. [1] Leon ta mutu a ranar Alhamis, 15, Agusta watan, 1996 tana da shekaru 51 a Nigtevecht.[1][2]

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 1.5 1.6 "Leon, Ruth Naomi". www.biografischportaal.nl (in Holanci). Retrieved 2017-11-23.
  2. "Oprichters – Mama Cash History". history.mamacash.nl. Retrieved 2017-11-23.