Tarihin Waliyi dan Marina

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
TARIHIN WALIYI DAN MARINA

Tarihin Wali Dan Marina unguwar Masanawa da ke cikin birnin katsina unguwa ce mai dimbin tarihi kuma sananniya ce saboda a nan ne manyan Waliyai masu karamomi suka wanzu a karni na goma sha bakwai (17th Century).

Waliyan su ne Wali Dan-Marina da kuma Wali Dan-Masani. Tarihi ya nuna cewa cikakken sunan wali Dan Marina shi ne Muhammad Ibn al-Sabbagh. Tarihi ya nuna cewa mahaifinsa balarabe ne wanda ya taso daga gabas ya kuma sauka a birnin Katsina da ke arewacin Najeriya a gidan wani malami kuma attajirin arini mai suna Kayaba. Wannan marini an ce shi ne yake yi wa Sarkin Katsina na wancan lokacin Mamuda da iyalinsa rinin tufafinsu.

Ana nan sai wata rana mahaifin wali Dan-marina ya ga ‘yar Sarki Mamudu wadda ake kira da Baraka, ya ji kuma ta kwanta masa. A haka ne ya nemi aurenta, sai aka aura masa ita a kan sadaki zinare shida, suka kuma tare a gidan kayaba.[1] A ciki akwai karamar karatun alkur'ani mai girma, inda ya kasance yana shan Kan malaminsa tun kafin a koya masa. Akwai kuma wata takaddama data tashi a gari game da watan azumin Ramadana, wasu suna cewa watan ya kare, sai aje a duba watan Sallah, wasu kuwa na cewa bai kare ba sai washegari. To, da aka taru sai ba'aga wata ya tsaya ba. Sai Wali dan Marina ya fere fasasshiyar kwarya, yayi mata siffar wata, sannan ya jefa sama. Sai kuwa ta tsaya, ya nunawa mutane yace ga wata san. Sai kowa ya yarda wata ya tsaya. To shikuma Wali Dan Masani sai ya musanta, yace wannan ba wata bane. Sai Yayi addua, ya mika hannu sama, sai gashi ya riko watan. Ya nunawa mutane, suka kuma yadda. Wannan itace takaddamar data shiga tsakanin waliyyai biyu, suka nunawa mutane karama.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]