Jump to content

Tarihin Wukari

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Wukari kamar yadda aka fi kiranta, ita ce shelkwatar masarautar Wukari. Asalin sunanta shi ne Ukari, wacce kuma kalma ce ta Jukunanci, wacce ke da ma’ana ta ka fifita (you have surpassed). Masarauta ce da aka kafa ta a shekarar 1596 bayan rushewar Daular Kwararrafa.

Bayan rushewar Daular Kwararrafa wacce ke da helikwata a Api , sai Jukunawa waɗanda su ke tun asali su ne ke shugabanta waccar daula ta Kwararrafa suka matsa gaba zuwa wannan bigire, suka kafa garin da a yanzu ake kira Wukari. Ita kuwa wannan kalma ta Wukari, asalinta shi ne Ukari, wacce kuma kalma ce ta Jukunanci mai ma’ana ta ka fifita (you have surpassed). Sarkin Jukunawa na 40, Aku Uka Katakpa, shi ne ya jagoranci wannan ƙaura a cikin shekarar 1596 (Adamu, 2016; Oleyede, 1996). Dukkan wanda ke shugabantar wannan masarauta, shi ake kira Aku Uka , kalmomin da ke da ma’ana ta sarkin da ya fifici kowane sarki a duniya; wato sarkin da ya fi kowane sarki a duniya (Adamu, 2016).[1]

Wannan gari shi ne ya zamo tubulin canjin tarihin Jukunawa, ya kuma zama sabuwar helikwatar daular Jukunawa zalla, a maimakon daular haɗaka ta Kwararrafa da Jukunawa suka shugabanta wacce ke ƙunshe da mabanbantan yarurruka.

Tun da fari, garin Wukari an kafa shi ne unguwa-unguwa, wanda kuma kowace

unguwa mazauna cikinta kusan zuriya guda ce. daga cikin irin wannan

unguwanni akwai Go-Ndoku , wacce ke nufin gidan sarki ko fadar sarki. Sai kuma

wasu unguwannin da suka haɗa da Kinda Kuvyo, Adikyu-Gashi, Ndo Abonta,

Kwanse, Ndo-Nwugye, Tsupando, da sauransu (Adamu, 2016).[2]

Gari ne wanda ke kewaye da ganuwa da kuma ƙofofi guda bakwai duk da cewa a

yanzu, ƙofar arewa ce kaɗai ta saura da jama’a ke amfani da ita; wacce kuma a

zamanin baya, mafita ce ta gawarwakin jinin sarauta. Haka nan kuma a tsakiyar

garin akwai tsohuwar kasuwar da tun da aka kafa garin take.

Sahun farko na sauran yarurruka mazauna wannan gari na Wukari akwai

Gobirawa, waɗanda kasuwanci ya kai su garin kuma suke zaune kusa da fadar

sarki, wanda har ta gai ga shugabansu mai suna Maiwuya ya auri ‘yar sarkin

Wukari na wancan lokacin abin da ya bashi damar da aka yi masa sarkin

kasuwar wukari, wanda ke da alhakin tattara haraji.

Haka nan kuma a shekarar 1932, a zamanin Aku Amadu Agbumanu, wasu

jama’a daga Sakkwato sun ƙaura zuwa Wukari, biyowa bayan tuɓe sarkin

Musulmi Muhammadu Tambari da aka yi, wanda kuma ya yi gudun hijira zuwa

garin na Wukari, inda a can ya rasu kuma aka binne shi a can. [3]A yanzu haka

sauran zuriyarsa suna zaune a wannan gari na Wukari a wata unguwa da ake

kira Unguwar Sakkwato wacce ke daura da Akata.

Bayan zamowar wannan gari na Wukari helikwatar masarautar Jukunawa, shi ne

kuma helikwatar ƙaramar hukumar Wukari a ƙarƙashin jahar Taraba. Yanzu

haka wannan gari yana da ci gaban da har ta kai ga yana da jam’o’i guda uku da

kuma sauran manya da ƙananan makarantu.

Daga farkon kafa wannan gari zuwa yau, sarakuna ishirin da huɗu ne suka

shugabance shi. na farkonsu shi ne Angyu Katakpa (1596 – 1615), sai kuma

na ƙarshe wanda har yanzu yake kai (Dr.) Shekarau Angyu Masa-Ibi, Kuvyo II (1976 zuwa yau).[4]

  1. Adamu Ɗ. A. (2016). Shekarau Angyu Masa-Ibi, An Autobiography of the 24th Aku-Uka, as Told to Ɗanjuma A. Adamu. An buga a Able Productions tare da haxin Guiwar Animation Books.
  2. Oluyede I.O. (1996). Shaped by Destiny, A Biography of (Dr.) Shekarau Angyu Masa- Ibi, Kuvyo II, The Aku Uka of Wukari. University of Ilorin.
  3. Oluyede I.O. (1996). Shaped by Destiny, A Biography of (Dr.) Shekarau Angyu Masa- Ibi, Kuvyo II, The Aku Uka of Wukari. University of Ilorin.
  4. Tattaunawa da (Dr.) Shekarau Angyu, Masa-Ibi, Kuvyo II, Aku Uka na Wukari, a ranar Asabar 19/08/2017, a fadarsa da ke Wukari