Jump to content

Tattalin arziki

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
tattalin arziki
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na social system (en) Fassara
Karatun ta ikonomi, economic anthropology (en) Fassara da Mai tattala arziki
Hashtag (en) Fassara economy
wani yanayi na bunkasa tattalin arziki a yayin kullen Korona virus
hoton masana tatalin arziki

Tattalin Arziki (Economy) ya dogara ne a kan samar da abinci da sutura da ayyuka, kiwon lafiya da Ilimi da gine-gine da sauransu da kuma rarraba su da cinikayyarsu har zuwa ga amfani da su ga al'umma. Tattalin arziki shi ne bunkasa da aiwatarwa da habaka ayyukan dake kawo cigaban kasa ta hanyar dogara a kan fitar da amfani daga ayyukan da mutum ke yi don amfanar kansa da kuma kula da su. Abubuwan dake habaka tattalin arzikin kasa sun hada da mutane, kasuwancin da ma'aikatu da gwamnati. Ayyukan tattalin arziki ya fara ne tun daga cinikayya, wato a sanda mutane biyu suka kulla yarjejeniyar cimma ciniki a kan wani abu da ake so, ta hanyar amfani da kudi ko wani abu mai daraja kamar zinari da azurfa da tagulla da dai sauransu. Duk da yake ana ganin cinikayya ta kudi kawai wani karamin abu ne idan ana magana a kan tattalin arzikin kasa.

Tattali arziki na samun himma ne tun daga samar da ayyuka ko abubuwan da ke amfani da albarkatun kasa ko ma'adinai da aikin dan'adam da sa jari. Amma haka ya canja sanadiyar canjin rayuwa, da kuma cigaban fasahar dan'adam wurin amfani da injina masu sarrafa kansu. Haka ya kawo samun sauki da saurin aikata ayyukan da kuma rage kudin da ayyukan Kasa. Haka nan kuma samun cigaba wurin kirkiran sabbin abubuwan da sabbin hanyoyin aiki da sabbin hanyoyin gabatar da ayyuka, manya-manya kasuwanni, kasuwannin da suka tattari abubuwa daban-daban, an kuma sami karin kudin shiga.

Tattalin arziki yana samun nasara ne sanadiyar ayyukan al'adun al'ummah, martabarsu da ilimin su da fadadar fasaharsu da tarihinsu da tsarin al'ummarsu da tsarin tafiya da siyasarsu da dokokinsu. Har wayau, da kuma irin yanayin kasar da ma'adinan kasa da yanayin rayuwar halittun kasar, wadannan su ne ke bayar da cikkakiyar samun habakar arzikin kasa. Kuma wadannan abubuwan suke bayar da guri da abubuwan da arziki ke cigaba da su sannan ya tsarasu a kan amfanuwar kasa da al'ummarta.

Akwai tattalin arziki da ya dogara kacokaf a kan kasuwanci, kuma yana gudana ne a kan cinikayyar ayyuka ko kayayyaki tsakanin mutane, ta hanyar samar da su da kai su kasuwanni domin cinikinsu da kudade ko da wani abun da aka kayyade mai daraja.

Akwai tattalin arziki da ya dogara a kan bayar da umurni daga 'yan'siyasa kaitsaye da kula da yadda ake samar wa 'yan kasa da ayyuka ko kayayyaki da kuma yadda za a sayar da su da rarraba su.

Akwai tattalin arziki da ya dogara a kan ma'adinan kasa, da sanya al'umma a cikin gudanarwarsu. Abdulrauf Lawan Saleh Sarkin Yakin Arewa ne ya wallafa.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]