Tenille Dashwood
![]() | |
---|---|
![]() | |
Rayuwa | |
Haihuwa |
Boronia (en) ![]() |
ƙasa | Asturaliya |
Mazauni |
Orlando (mul) ![]() |
Ƴan uwa | |
Ma'aurata |
Riddick Moss (en) ![]() |
Sana'a | |
Sana'a |
professional wrestler (en) ![]() |
Nauyi | 60 kg |
Tsayi | 1.65 m |
Sunan mahaifi | Emma, Tenille Dashwood, Tenille Tayla, Valentine, Tenille Williams da Emmalina |
IMDb | nm3798107 |
tenilledashwood.net |

Tenille Averil Dashwood (an haife ta ranar 1 Maris 1989) ƙwararriyar yar kokawa ce ta Australiya kuma mai bada shawarwarin taafiye-tafiye.[1] An fi saninta da zamanta a WWE, a ƙarƙashin sunan zobe Emma. An kuma san ta da lokacinta tare da kungiyoyin wasan kokawa masu suna Ring of Honor (ROH) da kuma Impact Wrestling, inda ta yi wasa da sunanta na gaskiya.
Rayuwar Farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Dashwood kuma ta girma a Boronia, Victoria, wani yanki na Melbourne.[2] Tana da babban yaya mai suna Jake, wanda ya gabatar da ita ga ƙwararrun kokawa.[3] Ta ambaci Stone Cold Steve Austin, Trish Stratus da Lita a matsayin kwarin gwiwarta a kokawa. Ta sadu da Dustin Rhodes a shekarar 1997 kuma, tana da shekaru 13 a 2002, ta sadu da Stratus a Yawon WWE na Duniya don Dumamar Yanayi: Melbourne.[4]
Rayuwarta
[gyara sashe | gyara masomin]A ranar 30 ga Yuni 2014, an kama Dashwood a Hartford, Connecticut. Ta iso bayan fage, amma ba ta fito a cikin shirin Raw wanda aka watsa kai tsaye a daren ba.[5] 'Yan sanda sun sake ta bayan ta amince ta bayyana a Kotun Community Hartford,[6] wanda ta yi washegari a ranar 1 ga Yuli. A cewar lauyanta, ta manta da biyan kudin wata harka ta iPad a lokacin da ta yi amfani da na'urar tantance kanta wajen siyan ta a Walmart. 'Yan jaridan Bryan Alvarez da Sean Ross Sapp sun tattauna da manajojin kare asara na Walmart wadanda, bayan sun binciki lamarin, sun tabbatar da cewa Dashwood ta biya kudin sayan ta, sai dai siyayya daya da ba'a tantance da kyau ba. Ma’aikatan sun soki wannan kamun, inda suka bayyana cewa ma’aikacin ya tunatar da ita cewa, abu daya ba a duba shi yadda ya kamata ba, musamman idan aka yi la’akari da tsadar kayan da aka manta.[7] Kotu ta umarce ta da ta yi hidima ga gari na kwana daya,[8] da kuma karatu ta yanar gizo, daga bisani aka yi watsi da karar.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://m.imdb.com/name/nm3798107/
- ↑ [3]Walter, Denis (11 June 2014). "WWE's Tenille Dashwood aka 'Emma'". 3AW Afternoons. 3AW.
- ↑ [5]"Emma". Online World of Wrestling. 30 May 2023. Archived from the original on 30 October 2022. Retrieved 29 October 2022.
- ↑ [8]Saxton, Byron (5 September 2013). "NXT 10-Count: Emma". WWE.com. Archived from the original on 24 December 2014. Retrieved 10 December 2014.
- ↑ "Emma already finished with court; her lawyer says arrest was due to a mistake". Cageside Seats. 1 July 2014. Archived from the original on 8 September 2017. Retrieved 7 September 2017.
- ↑ Wenzel IV, Joseph. "WWE Diva Emma arrested before 'Raw' in Hartford". WFSB. Archived from the original on 9 July 2014. Retrieved 3 July 2014.
- ↑ Mike Dyce (5 July 2014). "New information on Emma's arrest and situation". fansided.com. Archived from the original on 6 March 2018. Retrieved 6 March 2018.
- ↑ "Latest reports on Emma's arrest before WWE Raw on June 30, 2014". Cageside Seats. 1 July 2014. Archived from the original on 8 September 2017. Retrieved 7 September 2017.